You are here: HomeAfricaBBC2021 03 29Article 1217851

BBC Hausa of Monday, 29 March 2021

Source: bbc.com

Muhawara ta kaure a Facebook kan haihuwar ƴaƴa barkatai a Arewacin Najeriya

Tun a farkon wannan makon nan muhawara ta sake kaurewa game da batun yadda mutane musamman Hausawa a arewacin Najeriya ke haihuwa barkatai ba tare da la'akari da ƙarfinsu na iya ɗaukar dawainiya ko tarbiyya ƴaƴansu ba.

Muhawara game da yadda malam Bahaushe yake haihuwa barkatai ba sabon abu ne, sai dai lamarin ya dauki sabon salo sakamakon yadda ake alakanta wasu matsalolin rashin tsaro da arewacin Najeriya ke fuskanta da haihuwa barkatai.

Bayanai sun nuna cewa galibin magidantan da kan haifi 'ya'ya barkatai marasa karfi ne, lamarin da kan sa su yi watsi da dawainiyar ciyarwa da shayarwa da makaranta da ma tarbiyya da take kansu.

Galibin lokuta iyayen irin waɗanan yara na aikawa da su almajiranci ko bara ko talla, idan mata ne kuma a aurar da su da wuri ba tare da ba su ilimi da ɗora su a kan turbar da ta dace ba.

Wasu suna danganta haihuwa barkatai da dimbin matsalolin da ake fama da su yanzu haka a Najeriya irin su rashin tsaro da ƙaranci ilimi da barace-barace da karuwar talauci.

A wannan lokaci ma abin da galibin mutane ke tsokaci a kai musamman shafukan sada zumunta kamar Facebook shi ne yadda ake haihuwar ba tare da iya bada tarbiya ko kula da yaran da ake haifa ba.

Me ake cewa a Facebook?

Masu tafka muhawarar na bayyana mabambanta ra'ayoyi kan alfanun tara yara da akasin haka, sai dai galibi damuwar da suke nunawa ita ce a kan tarbiyya da karfin ba da cikakkiyar kulawa ga iyali.

Wasu na cewa akwai bukatar wayar da kawuna da ilimantarwa kan koyarwar addini a kan hakkin yara yayin da wasu ke ganin bai kamata mara karfi ya auri.

Abubakar Widi-Jalo na ganin yawanci rashin zaman lafiya da rikicin da ake tafkawa a gidan namiji mai mata sama da ɗaya na da nasaba da tsarin rayuwa da zaman da ake. Ya bada misali da mara hali da ya aure mace sama da guda yana mai cewa dole a rinka kunce da aikata mugan laifuka.

Ƙarin haske

A Najeriya, an dade ana ta kai kawo dangane da yadda za a yi amfani da yawan jama'a domin ci gaban kasar. Kusan kowace gwamnati takan yi tsare-tsare dangane da yadda za ta tafiyar da al'umma, musamman ma wajen samar da kyakkyawan yanayin rayuwa, wanda ya shafi tattalin arziki, ilimi, lafiya, muhalli, tsaro da sauransu.

Sai dai masu lura da lamura na ganin babbar matsalar ita ce rashin samar da dawwamammen tsari da zai kawo ci gaba ba tare da nuna son kai ba, lamarin da a karshe yakan sa manufofin gwamnatin ba sa dorewa.