You are here: HomeAfricaBBC2021 04 09Article 1227604

BBC Hausa of Friday, 9 April 2021

Source: BBC

Ministan Shari'a ya musanta cewa Atiku Abubakar ba ɗan Najeriya ba ne

Ministan Shari'a na Najeriya Abubakar Malami Ministan Shari'a na Najeriya Abubakar Malami

Ministan Shari'a na Najeriya ya musanta wasu rahotanin da kafafen watsa labarair suka bayar cewa ya fada wa wata kotu cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar bai cancanci tsayawa takarar shugabancin ƙasar ba, don ba haifaffen ɗan Najeriya ba ne.

Abubakar Malami ya ce shari'ar da ake magana a kai wata ƙungiya ce mai suna "Incorporated Trustees of Egalitarian Mission for Africa" (EMA) ce ta shigar da ita tun a shekara ta 2019 kuma shi ma yana cikin wadanda ake kara.

Ministan ya yi martanin ne bayan ce-ce-ku-cen da ake ta yi sakamakon labarin da wasu jaridun Najeriya suka wallafa cewa Abubakar Malami ya ce Atiku Abubakar bai cancanci takarar shugabanci Najeriya ba saboda lokacin da aka haife shi garinsu na ƙarƙashin Jamhuriyar Kamaru.

Ɗaya daga cikin jaridun Najeriya Pulse ta rawaito cewa ministan na cewa an haife Atiku a garin Jada na Adamawa a 1946 a lokacin garin yana karkashin ikon kasar Kamaru - sai bayan shekara ta 1961 garin ya koma karkashin Najeriya.

Jairday ta ambato ministan yana cewa bisa wannan dalili tsayawar Atiku takara ta saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Wannan batu ya ja hankali sosai a faɗin ƙasar musamman a kafofin sada zumunta inda mutane suka rinka bayyana mabambanta ra'ayi.