You are here: HomeAfricaBBC2021 03 22Article 1211542

BBC Hausa of Monday, 22 March 2021

Source: BBC

Liverpool ta musanta yarjejeniya da Barcelona, Arteta na son rike Odegaard

Dan wasan tsakiya Georginio Wijnaldum tare da kocin Liverpool Klopp Dan wasan tsakiya Georginio Wijnaldum tare da kocin Liverpool Klopp

Liverpool ta ce ba ta san da wata yarjejeniya ba da Barcelona za ta dauki dan wasan tsakiya Georginio Wijnaldum, mai shekara 30 ba, kafin ta sayi dan wasan na kasar Holland. In ji jaridar Liverpool Echo.

Kociyan Arsenal Mikel Arteta ya ce Martin Odegaard shi ne jagoran 'yan wasan kungiyar, kuma ya nuna aniyarsu ta daukar dan wasan na real Madrid dan Norway mai shekara 22 ya zauna dindindin. In ji jaridar Mirror.

Juventus a shirye take ta ba wa Everton 'yan wasa hadi da kudi domin dawo da tsohon dan was anta nag aba dan Italiya Moise Kean mai shekara 21, kamar yadda Tutto Juve ta ruwaito daga Teamtalk.

Ita kuwa kungiyar Crystal Palace na harin sayen dan wasan baya ne na Juventus, dan Romania Radu Dragusin mai shekara 19. In ji Sun.

Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya kawar da duk wata yuwuwa ta cewa Hansi Flick zai maye gurbin Joachim Low a matsayin kociyan tawagar Jamus. In ji jaridar Welt ta Jamus.

Udinese's Mai Golan kungiyar Udinese, dan Argentina Juan Musso, mai shekara 26, na shirin watsi da duk wani tayi daga Inter da AC Milan, inda ya yanke shawarar tafiya Roma. Kamar yadda Todofichajes ta labarto.

An bai wa mataimakin mai horad da 'yan wasan Sheffield United Alan Knill damar tsayawa ya ci gaba da aiki a kungiyar bayan da Chris Wilder ya tafi. In ji jaridar Sheffield Star