You are here: HomeAfricaBBC2021 04 22Article 1239340

BBC Hausa of Thursday, 22 April 2021

Source: BBC

Lai Mohammed: Birtaniya tana yi wa Najeriya zagon-kasa a yaki da ta'addanci

Ministan watsa labaran Najeriya Lai Mohammed Ministan watsa labaran Najeriya Lai Mohammed

Ministan watsa labaran Najeriya Lai Mohammed ya yi zargin cewa kasar Birtaniya tana yi wa Najeriya zagon-kasa a yakin da take yi da ta'addanci.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya ambato Mr Lai Mohammed yana cewa matakin da Birtaniya ta dauka na bai wa wasu masu fafutukar ballewa daga kasar 'yan kungiyar IPOB mafaka "rashin mutunci ne da kuma zagon-kasa" ga Najeriya a yakin da take yi da ta'addanci.

Ya kara da cewa tuni Najeriya ta ayyana 'yan kungiyar IPOB a matsayin 'yan ta'adda don haka bai ga dalilin da zai sa Birtaniya ta nemi ba su mafaka ba.

"Idan ya tabbata cewa da gaske Birtaniya za ta bayar da mafaka ga 'yan IPOB da MASSOB da ake zargi ana musgunawa, lallai akwai matsala. Ba wai kawai an haramta IPOB a Najeriya ba ne, an kuma ayyana ta a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Don haka matakin da Birtaniya ta dauka na raini ne matuka ga Najeriya a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta. Kuma hakan zagon-kasa ne ga yunkurin da muke yi na yaki da ta'addanci," in ji Lai Mohammed.

Ministan ya kara da cewa matakin zai gurgunta tsaron kasar sannan zai raba kawunan 'yan Najeriya.

Mayakan IPOB sun dade suna fafutukar ballewa daga Najeriya, kasar da suka bayyana a matsayin tamkar gidan ajiye namun daji.

Kwanakin baya sai da rundunar 'yan sandan kasar ta dora musu alhakin kashe-kashen da ake yi wa jami'anta a kudu maso gabashi da kudu maso kudancin kasar bayan da suka kona ofisoshin 'yan sanda da wani gidan yari da ke birnin Owerri, sannan suka kubutar da daurarru.

Kazalika 'yan arewacin Najeriya da ke zaune a jihohin kudu maso gabas sun zarge su da kashe 'yan uwansu saboda nuna kiyayya.