You are here: HomeAfricaBBC2021 03 29Article 1218649

BBC Hausa of Monday, 29 March 2021

Source: www.bbc.com

Lafiya Zinariya: Matsalar karancin jini a tsakanin mata masu ciki

Wasu alkaluma da hukumar lafiya ta duniya ta wallafa a shafinta na intanet sun nuna cewa Najeriya na da matan da ke fuskantar karancin jini da suka kai kashi 49.79 cikin dari.

Haka kuma makwabtanta kamar su Nijar nata adadin ya kai kashi 49.5 cikin dari.

Sai Ghana mai kashi 46.39 cikin dari da kuma Kamaru mai kashi 41.41 cikin dari.

Alkaluman hukumar sun nuna cewa a duniya mace daya cikin kowace uku da ba su wuce shekarun haihuwa ba na fama da matsalar karancin jini a jiki.

Haka zalika kimanin mata masu ciki kashi 40 ne cikin dari ke fama da wannan matsalar, yayin da matsalar ta kuma shafi yara 'yan kasa da shekara biyar a duniya da kashi 40 cikin dari.

A cewar alkaluman hukumar wanda aka sabunta a shekarar 2017, kasar Yemen ta fi kowace samun matan da basu wuce shekarun haihuwa ba, da ke fama da karancin jinin, inda take da kashi 69.6 cikin dari.

Har wa yau a yankin na gabas ta tsakiya, kasar Saudi Arabiya na da kashi 42. 91 cikin dari na irin wadan nan mata.

Sai kasar Bahrain mai kashi 41.96 cikin dari.

Hukumar dai ta ce matsalar rashin isasshen jini a jikin mata masu juna biyu da ma wadanda basu wuce shekarun haihuwa ba, da kuma kananan yara, matsala ce da ta taba kowane sashe na duniya.

A yankin Asia, kasar Pakistan ta fi kowa yawan mata masu rashin isasshen jini a jiki, inda take da kashi 52 cikin dari.

Sai India, wadda ita kuma ke da sama da kashi 51 cikin dari a cewar hukumar. Yayin da kasar Cambodia kuma nata alkaluman suka kai kashi 46.78 cikin dari.

A nahiyar Afrika, kasar Gabon ta fi kowacce kasa wannan matsala, inda kashi 59.06 na matan da ke haihuwa kuma su ke fama da matsalar ta karancin jinin.

Sai kasar Gambia mai sama da kashi 57 ciki dari, yayin da Ivory coast ke da kusan kashi 53 cikin dari.

Sannan Congo na da mata masu wannan matsala kusan kashi 52 cikin dari, sai kuma Mali da ke da kashi 51 cikin dari.

Kasar Haiti da ke yankin Carrebean, tana da matan da ke da rashin isassashen jini da suka kai kashi 46.25 a cikin dari.

A cikin jadawalin hukumar, da ke dauke da sunayen kasashen duniya 186, tare da alkalumansu, Australia da Canada ne kadai kasashen da ke da mafi karancin masu wannan matsala.

Australia na da kashi tara ne kacal da dan dori cikin dari, yayin da ita kuwa Canada ke da kashi 9.53 cikin dari.

Latsa hoton da ke sama domin sauraren bayanin da Dr. Rukayya Dawud ta yi wa Habiba Adamu: