You are here: HomeAfricaBBC2021 03 06Article 1197667

BBC Hausa of Saturday, 6 March 2021

Source: BBC

Lafiya Zinariya: Halin da ma'aikatan lafiya ke ciki a annobar cutar korona

Najeriya ta karbi alluran riga-kafin cutar korona kusan miliyan hudu Najeriya ta karbi alluran riga-kafin cutar korona kusan miliyan hudu

Ku latsa lasifikar da ake sama don ssauraron cikakken shirin wanda Habiba Adamu ta gabatar.

Wani bincike da aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta The Lancet ya gano cewa, ma'aikatan kiwon lafiya na fuskantar karin barazanar kamuwa da cutar Covid-19.

Sai dai hukumomi a fadin duniya, sun tunkari wannan kalubale ta hanyar fara yi musu riga-kafin cutar.

A ranar 2 ga watan Maris 2021 ne, Najeriya ta karbi alluran riga-kafin cutar kusan miliyan hudu.

Kuma su ne kashi na farko daga cikin allurai miliyan 16 da ake sa ran kasar za ta samu a watanni masu zuwa.

Kamar a wasu kasashe, ma'aikatan lafiya na sahun farko da hukumomin kasar suka ce za a fara yi wa allurar riga-kafin Covid-19.

Hukumomi a Najeriya sun ce, daga watan Fabairu zuwa watan Agustan shekarar 2020, an samu ma'aikatan kiwon lafiya 800 da suka kamu da cutar korona a kasar.

Sai dai wasu alkaluman da BBC ta samu sun nuna cewa, zuwa farkon watan Maris 2021, an samu a ƙalla likitoci 1,200 da suka kamu da cutar a kasar, yayin da 45 kuma suka rasa rayukansu.

Wasu daga cikin kasashen Afrika da suka samu karbar alluran riga-kafin, sun hada da Ghana da Senegal da Rwanda da Kenya da kuma Ivory Coast.

Yayin da Babban Bankin Duniya ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa ya shirin samar da kudade cikin gaggawa domin tallafawa kusan kasashe 30 a nahiyar ta Afrika domin samun alluran riga-kafin.