You are here: HomeAfricaBBC2021 06 08Article 1281139

BBC Hausa of Tuesday, 8 June 2021

Source: www.bbc.com

Kylian Mbappe zai ci gaba da zama a PSG — Al-Khelaifi

Dan wasan Paris St Germain, Kylian Mbappe zai ci gaba da taka leda a Ligue 1 in ji shugaban kungiyar, Nasser Al-Khelaifi.

Shugaban ya mayar da martani ne kan rade-radin da ake yi kan makomar dan wasan tawagar Faransa a PSG.

Mbappe, wanda ya ci kwallo 42 a dukkan fafatawa a kakar nan a PSG, yana da sauran yarjejeniyar da za ta kare a karshen Yunin 2022.

Ana ta alakanta dan kwallon tawagar Faransa da cewar zai koma Real Madrid da taka leda daga kakar badi.

Al-Khelaifi ya sanar wa da jaridar L'Equipe cewar ''Bari na fayyace, Mbappe zai ci gaba da wasa a Paris, ba za mu sayar da shi ba, ba za mu bari ya bar PSG a matakin wanda bai da yarjejeniya da mu ba.

Mbappe yana da dukkan abubuwan da yake bukata a Paris, ''Ina kuma zai je? wacce kungiyace a matakin cimma buri da za ta yi kafada da PSG a wannan lokacin?

Abin da zan ce komai yana tafiya yadda ya kamata, ina fatan zamu kulla sabuwar kwantiragi da shi nan gaba kadan.

''Nan birnin Paris ne, kuma kasarsa ce, yana da abinda ya sa a gaba, ba kawai kwallon kafa ba, har da daga darajar gasar Ligue 1 da kasarsa da kuma birninsa.''

PSG ta kammala kakar bana da kofi daya shi ne French Cup, bayan da ta kasa lashe Ligue 1 da tazarar maki daya tsakaninta da Lille, wadda ta ci kofin bana.

An kuma yi waje da PSG daga gasar Champions League a karawar daf da karshe a bana, bayan da ta kai wasan karshe a bara da Bayern Munich ta yi nasara da ci 1-0.