You are here: HomeAfricaBBC2021 03 31Article 1220461

BBC Hausa of Wednesday, 31 March 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Yarjejeniyar Messi, Aguero, Lukaku, Kane da Konate

Dan kwallon Argentina da Barcelona Lionel Messi Dan kwallon Argentina da Barcelona Lionel Messi

Manchester City za ta nemi sayen dan wasan gaba na Tottenham, Harry Kane mai shekara 27, idan jagorar Premier ta kasa samun Erling Braut Haaland na Borussia Dortmund a bazarar nan. Jaridar The Times ta ruwaito

Haka kuma Manchester City din dai da Chelsea za su iya karkata ga neman Romelu Lukaku na Inter Milan, mai shekara 27, dan Belgium idan hakarsu ta kasa cimma ruwa wajen sayen Haaland, mai shekara 20, in ji jaridar Eurosport

Sai dai ana ganin City na da kwarin guiwar samun Haaland, dan kasar Norway a bazarar nan domin maye gurbin Sergio Aguero. (Manchester Evening News)

Ita kuwa Manchester United tuni har ta nuna sha'awarta ta daukar Aguero, mai shekara 32, wanda ya fara tattara kayansa domin barin abokan hamayyar United din, Man City a bazarar nan, yayin da sauran manyan kungiyoyi ma irin su Chelsea da Inter Milan da Paris St-Germain ke sha'awarsa. Ruwayar Foot Mercato, daga jaridar Star

Duk da cewa ana ganin Barcelona, ce ta fi damar samun nasarar janye Aguero, to amma kungiyar ba ta ba shi fifiko ba, domin ta fi son sayen Memphis Depay na Lyon, mai shekara 27 dan Holland, ko Haaland na Dortmund ko kuma ma Lukaka na Inter Milan, saboda dukkaninsu ba su kai Aguero shekaru ba. Mundo Deportivo ta Sifaniyanci ce ta ruwaito haka.

Sai dai kuma Lionel Messi, mai shekara 33 ya gindaya wa Barcelona sharadi kan ta dauki dan kasar tasa, Aguero, in har tana son ya amince da bukatarta ta tsawaita zamansa a cikinta. Wannan labari ruwayar Football Insider, ne

Bisa ga dukkan alamu tafiyar kyaftin din Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 25, Manchester City ba za ta yiwu ba, saboda farashin fan miliyan 100 da Villa ta sanya a kan dan wasan tsakiyar dan Ingila ya sa kungiyar ta Pep Guardiola ta ja baya. Ruwayar jaridar Telegraph.

Dan bayan RB Leipzig Ibrahima Konate, mai shekara 21, ya kammala gwajin lafiyarsa kuma ya yi nasara a shirin da dan wasan dan Faransa ke yi na tafiya Liverpool. Kamar yadda RMC Sport ta Faransanci ta labarto.

Kylian Mbappe, ya gaya wa shugabannin tawagar Faransa cewa ba zai samu damar zuwa gasar wasannin Olympic da za a yi ba na bazarar nan a birnin Tokyo, saboda yana son mayar da hankali a kan kungiya, saboda yana da sabuwar yarjejeniya da zai tattauna kan ci gaba da zama a PSG.

Liverpool da Manchester City da Real Madrid dukkanninsu na sha'awarsa. Kamar yadda Le Parisien, ta ruwaito daga jaridar Mirror.

Manchester United da Chelsea da kuma Paris St-Germain na ci gaba da zaman jiran neman sayen dan wasan tsakiya na Rennes Eduardo Camavinga, mai shekara 18, yayin da matashin dan wasan na tawagar Faransa ta 'yan kasa da shekara 21 ke shirin tafiya Real Madrid amma kuma yana son ya ga sai in Zinedine Zidane zai ci gaba da zama a Bernabeu. AS ta Sifaniyanci ta ruwaito

Arsenal da Leicester City da kuma Strasbourg na sha'awar dan wasan baya na Valenciennes Ismael Doukoure mai sheakara 17. Ruwayar Foot Mercato ta Faransanci

Juventus za ta sayar da Adrien Rabiot dan Faransa mai shekara 25 da kuma Aaron Ramsey dan Wales mai shekara 30 domin samun kudin da za ta sayo dan wasan tsakiya Houssem Aouar, mai shekara 22, daga Lyon, kamar yadda Calcio Mercato ta ruwaito

Juventus ta yi nasarar janye dan wasan tsakiya na Sassuolo Manuel Locatelli, mai shekara 23, wanda Manchester City da Real Madrid suka nuna sha'awarsu a kansa. Dan Italiyar zai koma Juventus a kaka mai zuwa. Tuttosport ta Italiyanci ce ta ruwaito labarin