You are here: HomeAfricaBBC2021 04 17Article 1235092

BBC Hausa of Saturday, 17 April 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Haaland, Milenkovic, Mbappe, Nketiah, Vinicius, Andersen

Dan wasan gaba na Borussia Dortmund dan Norway Erling Braut Haaland Dan wasan gaba na Borussia Dortmund dan Norway Erling Braut Haaland

Watakila Barcelona da Real Madrid su hakura da neman dan wasan gaba na Borussia Dortmund dan Norway Erling Braut Haaland saboda tsadarsa. Dan wasan mai shekara 20, na son duk kungiyar da za ta saye shi ta rika ba shi albashin fam miliyan 30 a duk shekara. (Jaridar Goal)

A shirye Manchester United take ta nuna bukatarta ta sayen dan wasan baya na Fiorentina dan kasar Serbia Nikola Milenkovic, to amma kuma kungiyar tasa ta Italiya na son akalla fam miliyan 38 a kan dan wasan mai shekara 23 (Jaridar Sun)

Paris St-Germain na matsa wa Kylian Mbappe kan ya sanya hannu a sabuwar yarjejeniyar tsawaita zamansa a kungiyar, to amma kuma dan wasan gaban na Faransa mai shekara 22 ba ya son zaman nasa ya yi tsawo sosai. (Jaridar L'Equipe ta Faransanci)

West Ham na cike da kwarin guiwar sayen dan wasan gaba na Arsenal na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21, Eddie Nketiah, mai shekara 21, a lokacin kasuwar 'yan wasa ta bazaran nan da ke tafe. (Jaridar Evening Standard)

Manchester United da Arsenal na sha'awar daukar matashin dan wasan tsakiya dan kasar Faransa Eduardo Camavinga, mai shekara 18, wanda ya yanke shawarar kin ci gaba da zama a Rennes. (Jaridar Marca)

Manchester United na son sayen dan wasan baya na Fulham da Denmark Joachim Andersen, mai sheakara 24, wanda yake zaman aro a Fulham daga Lyon. (Jaridar B.T ta Denmark)

Kociyan RB Leipzig Julian Nagelsmann ya yi watsi da rade-radin da ake yin a cewa ya tattauna da kungiyar Bayern Munich domin maye gurbin kociyanta Hansi Flick. (Jaridar ESPN)

Amma kuma kamar yadda wani labarin ya bayyana daga jaridar Sport Mediaset ta Italiya kungiyar ta Bayern na duba yuwuwar daukar Massimiliano Allegri a matsayin wanda zai gaji Flick. Allegri bas hi da wata kungiya da yake horarwa tun bayan da ya bar Juventus a 2019.

Barcelona za ta bar dan bayanta na Faransa Samuel Umtiti, mai shekara 27, ya tafi a bazaran nan, inda take duba yuwuwar daukar dan bayan AC Milan da Italiya Alessio Romagnoli, mai shekara 26, a matsayin wanda zai gaje shi. (Jaridar Mundo Deportivo ta Sifaniya)

Dna wasan tsakiya na Sassuolo da kuma tawagar Italiya Manuel Locatelli ya ce zai duba yuwuwar tafiya wata kungiya ta waje. Ana rade-radin dan wasan mai shekara 23 na son zuwa Manchester City. (Jaridar Corriere dello Sport ta Italiya)

Haka ita ma Arsenal za ta iya sake neman Locatelli, wanda shekara biyar baya ma ta taba nemansa. (Jaridar Football.London)

Barcelona na duba yuwuwar daukar dan wasan gaba na RB Leipzig dan Sifaniya Dani Olmo, mai shekara 22, wanda ya taso daga cibiyar renon 'yan kwallo ta Barcelonar. (Jaridar Sport)

Atletico Madrid na sha'awar sayen dan wasan tsakiya Nicolo Rovella mai shekara 19 wanda Juventus ta bayar da aronsa ga Genoa, tare kuma da dan wasan baya na Udinese, Nahuel Molina, dan Argentina mai shekara 23. (Jaridar Mundo Deportivo ta Sifaniyanci)

Wolves za ta nemi daukar dan wasan Benfica na gaba Carlos Vinicius, mai shekar 26 dan Brazil a bazaran nan, bayan da Tottenham ta ce ba za ta mayar da shi dan wasanta na dindindin ba daga aro. Labarin ya fito ne daga tashar talabijin ta TVI24 ta Portugal.