You are here: HomeAfricaBBC2021 04 03Article 1222954

BBC Hausa of Saturday, 3 April 2021

Source: bbc.com

Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Aguero, Haaland, Messi, Jorginho, Lacazette da Zapata

Chelsea ce kan gaba a cikin kungiyoyin da ke yunkurin daukar dan wasan Argentina Sergio Aguero idan ya bar Manchester City a bazara yayin da dan wasan mai shekara 32 yake son ci gaba da murza leda a gasar Firimiya Lig. (Mail)

Benfica ta kasar Portugal ita ce kungiya ta baya bayan nan da ke son daukar Aguero tun da aka sanar ranar Litinin cewa zai bar Man City a karshen kakar wasa ta bana. (Record, via Mirror)

Rahotanni sun ce Arsenal da Independiente, kungiyar kasar Argentina inda Aguero ya soma sana'arsa ta kwallon kafa, sun bi sawun kungiyoyi irin su - Barcelona, Juventus da Paris St-Germain - da ke son daukar dan wasan a bazara. (Sun)

Liverpool za ta "fafata da" Barcelona a yunkurinta na daukar dan wasan Lyon da Netherlands mai shekara 27 Memphis Depay, wanda za a sanya a kasuwa a bazara. (Marca)

  • Man City na son hada Messi da Haaland, Juventus ta matsu da Pogba
  • Messi ya tilasta wa Barca ta sayi Aguero, Man City za ta nemi Lukaku
Mahaifin dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland, Alf-Inge, da wakilinsa Mino Raiola za su halarci taro a London tare da Manchester City, Chelsea, Manchester United da kuma Liverpool ranar Juma'a game da yunkurin daukar dan kasar ta Norway mai shekara 20. Tuni mutanen biyu suka gana da Barcelona da Real Madrid. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Sai dai ana sa ran Liverpool za ta daina neman daukar Haaland yayin da a gefe guda ake tsammanin Chelsea ce kan gaba a a yunkurin daukarsa. (Football Insider)

Dan wasan gaban Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, ya gabatar wa shugaban Barca Joan Laporta cikakken jerin bukatun da yake so a cika masa kafin ya sabunta zamansa a Nou Camp. (Eurosport)

Dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 25, wanda yake zaman aro a Atletico Madrid, ya ce yana son komawa Kudancin Amurka bayan mutuwar mahaifiyarsa kuma yana son shiga kungiyar Boca Juniors ta kasar Argentina domin a cika alkawarin da ya yi wa mahaifinsa. (ESPN Argentina, via Goal)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce a bazara za a san makomar dan wasan aban Faransa Alexandre Lacazette, kuma a lokacin ne dan wasan mai shekara 29 - wanda ake alakantawa da Roma, Atletico Madrid da kuma Sevilla - zai shiga watanni 12 na karshen kwangilarsa ta yanzu. (Guardian)

Olympiakos na duba yiwuwar neman aron dan wasan Arsenal mai shekara 21 dan kasar Ingila Reiss Nelson. (Football London)

Dan wasan Arsenal mai shekara 23 Ainsley Maitland-Niles yana sa ran barin kungiyar a bazara idan ya kammala zaman aron da yake yi a West Bromwich Albion. (Telegraph)