You are here: HomeAfricaBBC2021 05 04Article 1250125

BBC Hausa of Tuesday, 4 May 2021

Source: www.bbc.com

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Sancho da Lewandowski da Lingard da Bale, Haaland da Doekhi

Leicester City da Everton na cikin ƙungiyoyin da ke shirin mika tayinsu kan ɗan wasan Brentford mai shekara 25, Ivan Toney. (Athletic, subscription required)

Shugaban Tottenham Daniel Levy zai bai wa sabon kocin ƙungiyar zaɓin sake cimma yarjejeniya da ɗan wasan gaba a Wales Gareth Bale, mai shekara 31, (Mail)

Borussia Dortmund za ta bar Jadon Sancho ya bar ƙungiyar kan £87m, a baya dai ta nemi sama da £100m kan ɗan wasan tsakiyar. Ana alakanta ɗan wasan mai shekara 21 da Liverpool da Manchester United. (ESPN)

A gefe guda kuma, shugaban Dortmund Hans-Joachim Watzke ya jadada cewa ba za su sayer da ɗan wasan su ba Erling Braut Haaland - da ake alakantawa da Manchester United, Liverpool, Manchester City, Chelsea, Barcelona da Real Madrid - a wannan bazarar. (Metro)

Newcastle United da ƙungiyar Italiya Atalanta sun nuna zawarci sosai kan ɗan wasan Vitesse Arnhem, mai shekara 22, Danilho Doekhi, wanda ake alakanatawa Norwich City, Fulham da ƙungiyar da ke buga firimiyar Scottish Rangers. (De Telegraaf - in Dutch)

Manajan Robert Lewandowski, Pini Zahavi zai matsawa Bayern Munich kan ta sake bai wa ɗan wasan na Poland kwantiragi mai kwaɓi, ko kuma ta sayar da shi ga kulob din da zai iya sayensa da tsada. (Bild - in German)

Kulob din firimiyar Ingila Watford na tattaunawa da Inter Milan da ɗan wasan Ingila, Ashley Young, mai shekara 35, kan komawarsa kungiyar da ta soma daga darajarsa. (Watford Observer)

Kungiyar Faransa Nice har yanzu tana sha'awar dauke dan wasan tsakiya Jesse Lingard, bayan rashin nasarar da tayi a baya kan ɗan wasan bai shekara 28 lokacin da ya koma West Ham zaman aro daga Manchester United a watan Janairu. (Sky Sports Italia, via Calciomercato - in Italian)

Newcastle United ta zaƙu ta cimma yarjejeniyar tsawaita zaman ɗan wasan Swiss Fabian Schar a kungiyar (Northern Echo)

Tottenham ta soma tuntubar Norwich da ɗan wasan Ingila ajin shekaru kasa da 21 da ke buga baya, Max Aarons, dan shekara 21. (Football Insider)

Boca Juniors ta cire ranta kan ɗan wasan Manchester United da Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 34, ta sanya sunan ɗan wasan da ke taka leda a Club America Roger Martinez a madadinsa. (TyC Sports, via ESPN - in Spanish)

Leeds ta dukufa wajen cimma burinta na dauko ɗan wasan tsakiya mai kyau a wannan kakar. (Football Insider)

Har yanzu Maurizio Sarri shi ne mutumin da Roma ke kwadayi domin mayer gurbin kocinta, Paulo Fonseca a wannan kakar. (Sky Italia - in Italian)

Lucas Vazquez na gab da sabunta yarjejeniyarsa da Real Madrid, sai dai har yanzu yana da zaɓi kan koma wa AC Milan idan aka gaza daidaitawa da shi, sannan babu batun da ake yi cewa watakil ya tsallaka ya koma Atletico Madrid. (AS)