You are here: HomeAfricaBBC2021 03 31Article 1220746

BBC Hausa of Wednesday, 31 March 2021

Source: bbc.com

Karen Shugaba Biden ya sake cizon wani ma'aikacin Fadar White House

Karen shugaban kasar Amurka ya sake cizon wani mutum, kwanaki kadan da dawowarsa daga atisaye a Delaware, bayan cizon wani ma'aikacin na daban a farkon watan nan.

Mai magana da yawun Uwar Gidan Shugaban Ƙasa Jill Biden ya ce "bisa fargabar abin da ka iya faruwa" likitoci sun duba wani ma'aikaci kafin ya koma aiki.

Major shi ne ƙarami daga cikin karnukan Shugaba Biden da ake yi wa laƙabi da German Shepherds kuma su ne karnukan aikin ceto na farko a Fadar White House.

"Kare ne mai ban sha'awa," in ji Joe Biden.

A ranar Litinin mai magana da yawun Shugaba Biden Michael LaRosa, ya yi tsokaci kan abin da ya faru a ranar Litinin din inda ya ce: "Har yanzu Major yana ci gaba da sabawa ne da muhallin da yake ciki kuma ya taɓa cizon wani a lokacin da yake wucewa."

Kafar talabijin ta CNN ta ruwaito cewa karen ya ciji wani ma'aikacin hukumar kula da wuraren shaƙatawa, abin da ya sa sai da ya dakata da aiki likitoci suka duba shi. Sai dai jami'an wurin shakatawar ba su ce komai game da hakan ba.

An dauke dukkan karnuka biyu na Shugaba Biden, wato Major da Champ mai shekara 13, zuwa gidansa da ke Wilmington, Delaware, bayan cizon da ya faru a ranar 8 ga watan Maris.

Wata majiya da ba ta so a bayyana ba ta shaida wa CNN cewa a lokacin da abin ya faru, Major yana ta yin tsalle da haushin ma'aikata da jami'an tsaron White House.

Amma Shugaba Biden ya ce Major yana kokarin sabawa da mutanen da yake gani a yanzu. "Kokarin kare kansa ya ke yi, idan ya karyo kwana ya ga mutane sama da biyu da bai san su ba," kamar yadda ya shaida wa shirin Barka da Safiya Amurka da tashar ABC ke yi.

Ya kara da cewa: "Kashi 85 cikin 100 na mutanen Fadar White House suna ƙaunarsa. Abin da kawai yake musu shi ne lashe kafarsu da kaɗa jelarsa. Amma na lura wasu mutanen na jin kare.''

A shekarar 2018 ne Biden ya karbo rikon Major, lokacin ya na dan kwikuyo, wanda shekararsa uku.

Yayin da shi kuma dayan karen Champ ya dade a Fadar White House tun yana karami, lokacin Shugaba Biden yana mataimakin shugaban kasa. Sai a farkon shekarar nan ya sake dawowa Fadar White House.

Join our Newsletter