You are here: HomeAfricaBBC2021 05 01Article 1247875

BBC Hausa of Saturday, 1 May 2021

Source: BBC

Jihar Neja: Yadda jama'ar gari ke yarjejeniya da 'yan bindiga don samun damar yin noma

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello

Al'ummomin wasu garuruwa na yankin karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja a Najeriya sun fara bin matakin yin sulhu da 'yan bindiga, don su sami zaman lafiyar da zai ba su damar yin aikin gona a daminar bana.

Shugabannin al'ummomin da na 'yan bindigar ne ke zama su kulla yarjejeniya, cewa maharan za su daina addabar garuruwan da hare-hare. Yayin da su kuma jama'ar garuruwan za su biya 'yan bindigar wasu kudade, da kuma sama masu ababen hawa da kayan masarufi. 

Jama'ar garuruwan dai sun ce, dole ce ta sa su bin wannan mataki na kulla yarjejeniya da 'yan bindiga, kuma sun dan fara ganin alamun sauki a halin yanzu.

Daya daga cikin mutanen yankin wanda jagoran matasan yankin ne ya shaida wa BBC cewa a gundumar Garmana akwai wasu unguwanni da dama da tuni sun yi nisa wajen tattaunawa da 'yan bindigar, da zummar nemar wa kansu zaman lafiya.

''Ya danganci kowacce unguwa, kowacce unguwa da nata tsarin yin sulhun, wasu sukan ba su kudi su ba su babura domin neman zaman lafiya'' in ji shi.

Wani mutumi da ke zaune a daya daga cikin wadannan garuruwan ya bayyana wa BBC cewa an bai wa 'yan bindigar Naira Miliyan biyu, kuma tuni sun fara ganin amfanin yarjejeniyar, domin mutane na shiga su fita a duk lokacin da suke so.

Jihar Neja dai na daya daga cikin jihohin Najeriya da suka fi fama da matsalar tsaro, gwamnatin jihar na cewa tana iya bakin kokarinta domin yaki da matsalar, amma wadannan mutane na cewa sun gaji da irin wannan alkawari, don haka dole su tashi su nema wa kansu mafita.

A makon da ya gabata ne dai gwamnan jihar ya bayyana cewa an samu bullar 'yan kungiyar Boko Haram a jihar, inda wasu bayanai ke cewa tuni ma sun kafa tutocinsu a wannan karamar hukumar ta Shiroro.

Ita dai gwamnatin jihar ta ce ba ta da masaniya a kan wannan yarjejeniya da mutane ke yi da 'yan bindigar, tana cewa tana aiki tare da gwamnatin tarayya domin ganin an shawo kan matsalar.