You are here: HomeAfricaBBC2021 06 10Article 1283260

BBC Hausa of Thursday, 10 June 2021

Source: www.bbc.com

IPOB: 'Abin da ya sa jagororin Igbo ba sa sukar ƴan awaren'

Rochas Okorocha, tsohon Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, tsohon Gwamnan jihar Imo

Tsohon gwamnan jihar Imo kuma ɗan majalisar dattijai a Najeriya, Sanata Rochas Okoracha ya ce akwai buƙatar gwamnati ta yi amfani da sarakuna wajen magance rikicin `yan a-ware a shiyyar kudu maso gabashin ƙasar.

Sanatan wanda ya fito daga yankin da ke fama da rikicin na ƴan aware, ya ce jagororin al'ummar Igbo ba sa goyon bayan abin da ke faruwa a yankin yanzu, ko da yake, ba sa iya fitowa su soki lamarin, saboda gudun fushin matasansu.

"Yawancin mutane suna da tsoro, ka fada kuma gobe a je a samu yaronka a kashe". in ji shi.

Ya dai yi zargin cewa akwai manyan masu rura wutar rikice-rikice a duk sassan Najeriya, kuma ya zama wajibi gwamnati ta taka musu burki.

Tsohon Gwamnan ya shaida wa BBC cewa a lokacin da kungiyar IPOB ta fara a kudu, an dauki lamarinsu kamar wasa, "yaran da ba su da aikin yi, suna neman a san da su amma abin mamaki ga shi ta zama matsala".

"Yawancin wadanda suke wannan abun idan ka dube su ba za ka ce suna da wata sana'a ba, ba a dauke su kamar za su zama abin damuwa ba". in ji Sanatan.

Ya bayyana cewa akasarin matasan da suke haifar da wannan rikicin suna kokawa ne da rashin ba su abubuwan more rayuwa kamar wuta da ruwa.

A cewarsa kiran da wasu bangarorin kasar ke yi na a bai wa IPOB damar ballewa daga Najeriya abu ne mara yiwuwa saboda yadda yan kabilar Igbo suke a warwatse a Najeriya.

Sai dai ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya gaza ta fuskar bibiyar mutanen da ya nada kan mukamai - "rashin zuwa baya ka duba yadda suke aiki, suna aiki tsakaninsu da Allah ko suna wasa da aiki".