You are here: HomeAfricaBBC2021 06 10Article 1283059

BBC Hausa of Thursday, 10 June 2021

Source: www.bbc.com

Hirar Buhari da Arise TV: Abu shida da shugaban Najeriya ya faɗa kan halin da ƙasar ke ciki

Shugaba Muhammadu Buhari Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana matsayin gwamnatinsa kan batutuwa da dama da suka shafi kasar a hirar da ya yi da gidan talabijin na Arise TV da safiyar ranar Alhamis.

An yi masa tambayoyi kan batutuwa da dama da suka hada da rigimar da gwamnatinsa take yi da shafin Twitter da matsalar tsaro a arewaci da kudancin kasar da batun 'yan IPOB da abin da zai mayar da hankali akai idan ya kammala mulkinsa.

Matsalar tsaro

Shugaban ya yi tsokaci kan batun da ya fi addabar kasar wato matsalar tsaro, inda ya ce daga bayanan da yake samu daga hukumomin tsaro akwai kwararan dalilai da ke nuna cewa an samu ci gaba, musamman bayan sauya shugabannin hukumomin.

"A arewa maso yamma, ba shakka mun tura karin sojoji zuwa jihohin da suka fi fama da wannan matsalar, kamar a Zamfara, mun hana hakar ma'adanai, su kansu yan kasashen waje mun hana su yin aiki a wannan waje, sannan ana ci gaba da kokarin ganin an kawo karshen matsalar", in ji shi.

A cewarsa: "Matsalar arewa maso yamma ita ce ta mutanen da ke da al'adu iri daya suna kashe juna. Za mu tafiyar da su ta hanyar da suka fi fahimta. Mun bai wa 'yan sanda da sojoji umarni da kada su raga musu. Idan aka kori mutane daga gonakinsu, za mu shiga cikin yunwa."

Ya kara da cewa "A arewa maso gabashin Najeriya muna samun nasara a kan Boko Haram, kuma alamu na kara bayyana da ke nuna cewa an kusa murkushe su."

Hare-haren makiyaya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna damuwa a kan yadda ake ci gaba da samun karuwar hare-haren ;yan bindigar da ake zargin makiyaya ne, inda ya ce dole kowa ya yi mamaki a kan yadda makiyayan da a baya ake ganinsu rike da sanduna ace su ne a yanzu suke dauke da manyan makamai suna kashe mutane.

Ya ce rungumar shirin da gwamnatinsa ta bullo da shi na samar da matsuguni ga makiyaya zai taimaka wajen kawo karshen matsalar da ake fama da ita.

''A cewarsa, a halin da ake ciki an cinye kusan dukkanin hanyoyin da makiyaya ke amfani da su wajen zirga-zirga daga jihohi zuwa jihohi, don haka shima wannan ya taimaka wajen kara ta'azzara matsalar tsaro.

An kashe kananan hukumomi

Buhari ya ce a halin da ake ciki an kashe kananan hukumomi baki daya, basu da wani tari, basa iya yin komai a kashin kansu, hatta kudin da ake basu a halin da ake ciki basu da ikon tasarrafi da shu.

''Idan da ana ba wa karmar hukuma Naira Miliyan 300 domin ta yi wani aiki, a yanzu ba a bata abunda ya kai Miliyan 100 ma, wannan fa shine halin da kananan hukumomin ke ciki'', inji shi.

Ko da yake bai fadi shirin da gwamnatinsa ke yi na ganin kananan hukumomin su rabauta da yancin tafiyar da harkokinsu ba, sai dai ya ce idan aka ci gaba da tafiya a haka fatan da ake da shi na ganin an samar da ci gaba tun daga kasa na iya gamuwa da cikas.

Hare-haren IPOB

Batun kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra na IPOB, na cikin batutuwan da suka fi jan hankali a halin da ake ciki a Najeriya, musamman bayan kalaman da shugaban ya yi a baya bayan nan, inda ya ce ''za mu yi musu magana da irin yaren da suke ji.

Sai dai shugaban ya sake nanata batun da ya yi, harma ya kara da cewa za mu shirya yan sanda da sojoji domin su yi musu magana da irin yaren da suke ji.

Akwai buakatar a zuba ido don ganin ko me nanata maganar da shugaban ya yi zai haifar, musamman ganin yadda kasashen duniya suka yi masa caa !, a kan batun a baya.

Yaushe zai yi sulhu da Twitter?

Da aka tambaye shi kan lokacin da za a kawo karshen haramcin da aka yi na amfani da Twitter a kasar, Shugaba Buhari ya ce bazai ce komai ba a kan wannan batu, ko da yake ya amsa da cewa: "Twitter? Na bar wa kaina sanin hakan." Daga nan ya yi murmushi ya ja bakinsa ya yi gum.

'Abin da zan mai da hankali bayan na sauka'

Wata tambaya da aka yi wa shugaba Muhammadu Buhari ita ce ko me zai maifa hankali a kan da zarar ya sauka daga kan mulki la'akari da yadda mulkinsa ya taho gangara.

Shugaban ya amsa da cewa ''Kamar yadda ka sani ina da gona ta ina da shanuna, don haka zan rika zuwa can wajensu a kullum, sannan zan samawa kaina abubuwa da yawa da za su dauke hankalina''.

Sai dai ya ce kafin nan zai maida hankali wajen inganta batutuwa uku da suka shafi tsaro da tattalin arziki da kuma manyan ayyuka.