BBC Hausa of Wednesday, 12 October 2022
Source: BBC
Hukumomin Eritrea sun tsaurara daukar sabbin sojoji tare da farautar matasan da ke buya don kada tursasa musu shiga sojin a fadin kasar, yayin da yakin da ake yi a yankin makwabciyar Ethiopiar wato Tigray ke kara tsananta. Daukar ta wannan karon ta fi tsanani kasancewar hatta mata ma ba a kyale ba, inda ake tsare iyaye manya maza da mata a yunkurin da ake yi na tabbatar da tilasta ‘ya’yansu da suka boye don kada a shigar da su sun dawo sun mika wuya, kamar yadda kafofi da dama a kasar ta Eritrea suka gay awa BBC. Kafofin sun sheda wa BBC hakan ne da sharadin boye sunansu kasancewar Eritrea kasa ce da ke da tsanani kan kusan komai da ya shafi rayuwar jama’a. "Ganin yadda da yawa matasa suka yi watsi da kiran zuwa su shiga sojin, hukumomi sun tsananta kamen,’’ kamar yadda wata kafa ta ce. Kafar ta yi kari da cewa , hatta mata ma, wadanda mazajensu suka gudu ana tsare su. An kafa shingayen bincike a kan manyan tituna kuma an fadada bincike a birane da kauyuka. A babban birnin kasar Asmara, ana kama mutane a tituna, yayin da hukumomi ke rufe gidaje a yankunan karkara da dama, inda suke kwace shanu tare da cin mutuncin dangin da aka samu wani nasu ya gudu, kamar yadda wani ya shaida wa BBC. BBC ta tuntubi gwamnatin Eritrea domin jin ta bakin hukumomin . A makon da ya gabata ministan yada labarai na kasar Yemane Gebremeskel ya ce an kira wasu ‘yan kalilan daga cikin sojin ko-ta-kwana, yana mai musanta rahotannin cewa gaba dayan al’ummar kasar ne ake kokarin turawa yakin. Wasu masu lura da al’amura na bayyana yakin na kusan tsawon shekara biyu, wanda kusan ya shafi dukkanin yankunan Ethiopia da ke da iyaka da Tigray, a matsayin wanda aka fi zubar da jini a cikinsa kan yakin Ukraine. To amma kuma a iya cewa kafafen yada labarai ba su mayar da hankali sosai a kansa ba, saboda hukumomin Eritrea da Etiopia sun takaita tafiye-tafiye kuma kusan duk hanyoyin sadarwa da Tigray an katse su. Gwamnatin Eritrea mai karfa-karfa ta shiga yakin inda take goyon bayan dakarun Ethiopia da ke yaki da kungiyar masu fafutukar neman ‘yancin Tigray (TPLF). Ita da kungiyar mayakan Tigray ta shiga daukar mayaka ba ji ba gani a fadin yankin nata domin kara karfin rundunarta, bayan rugujewar tattaunawar zaman lafiya ta wata biyar a watan Agusta da kuma gazawar kungiyar tarayyar Afirka ta tabbatar da tattaunawar zaman lafiya. Jan hakali da Kalamai na sosa rai A watan Nuwamba na 2020 ne yakin ya balle sakamakon gagarumin sabani da aka samu tsakanin Firaministan Ethiopia, wanda ya ci lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel Abiy Ahmed da kungiyar fafutuka ta Tigray, TPLF, wadda ke da gwamnatin yankin, a kan tarin abubuwa da dama da suka hada da batun ko Ethiopia za ta ci gaba da tafiya a kan tsarin gwamnatin fedaraliya mai salon kabilu. Wata kafa a Eritrea ta gaya wa BBC cewa hukumomin Ethiopia sun rika kokarin ganin sun janyo hankalin jama’a ta hanyar sosa musu rai da kalamai a taruka inda suke danganta matakin sojin da suka dauka da wanzuwar kungiyar fafutuka ta Tigray, suna nuna bukatar ganin bayanta. Yakin na baya-bayan nan ya taso ne sakamakon gabar da aka dade ana yi tsakanin gwamnatin Eritrea da kungiyar ‘yan Tigray ta TPLF, wadda ta mamaye gwamnatin hadaka ta Ethiopia kafin zuwa zuwan Mista Abiy kan mulki a 2018. A karkashin TPLF, Ethiopia da Eritrea sun yi yakin kan iyaka wanda ya yi sanadiyyar mutuwar kusan mutum 80,000. Daga bisani wata kutun duniya ta musamman ta zartar da cewa Ethiopia ta mika yankin da ake rigima a kansa ga Eritrea, amma kuma gwamnatin da kungiyar TPLF ke jagoranta ta ki yarda ta yi hakan. To amma gwamnatin Eritrea ta kawace yankin jim kadan da fara yakin na baya-bayan nan a watan Nuwamba na 2020. A watan da ya gabata gwamnatin Eritrea ta gayyato sojinta na ko-ta-kwana masu kasa da shekara 55 kuma ta tura wasu daga cikinsu filin-daga. A ‘yan kwanakin da suka gabata an samu rahotannin fada a yankunan kan iyaka da dama wadanda suka hada da Adigrat, Rama, Shiraro da Zalambesa. To amma ‘yan Eritrea da yawa suna bijire wa gayyatar da hukumo,min kasar suke yi musu na gayyatarsu shiga aikin sojin a baya-bayan nan, suna cewa ba sa so su mutu a yakin da suke ganin bai zama dole ba. Hatta tsofaffi ma ba a bar sub a, ‘’ana tilasta musu zuwa yaki a yankuna da dama a yawancin lokaci, ana gudanar da aikin tilasta shiga sojin ba tare da wani tsari ba,’’ in ji wata kafa. Wani dan kasar ta Eritrea da ke waje ya bayyana damuwa a kan dan uwansa da kuma matar dan uwan nasa a Asmara. Y ace matar dan uwan nasa ta gudu da ‘ya’yanta zuwa kauyen iyayenta kuma yana fargabar cewa an tsare dan uwan nasa. Haka kuma hukumomin na kin bayar da tikiti na musamman na sayayya a kanti domin sayen kayan ,masarufi kamar sukari da mai a farashi mai sauki har sai iyalai sun amsa kiran da ake musu na zuwa su shiga soji, in ji wani. Buya cin amanar kasa ne Ana kawo mutane ofishin hukumomin yankunansu inda ake gargadinsu da cewa duk wanda ya boye ‘ya’yansa ko miji ko kuma ya taimaka waw ani ya buya ko ya gudu to hakan daidai yake da cin amanar kasa, in ji wani da BBC ta tattauna da shi. Ya kara da cewa, ‘’sun sa mutane cikin mawuyacin hali.’’ Wata mata a Eritrea ta ce ran mutane da dama ya baci saboda yadda yakin ya ci rayukan mutane ba kadan ba manya da kanana. Matar ta kara da cewa "Mutane na nuna adawarsu da yakin ta hanyoyi da damam amma tsarin jami’an tsaron kasar babu tausayi domin za su iya aikata duk wani ab una rashin Imani a kan jama’arsu.’’ Wani dan Eritrea da ke zaune a Denmark ya ce yana jin tsoron rayuwar iyalansa a can gida. Mahaifinsa mai shekara 67 sojan ko-ta-kwana wanda aka sa shi aiki a yankinsa, ko da yake zuwa yanzu ba a tura shi fagen daga ba. Mutumin ya fi damuwa da ‘yar uwarsa mai shekara 23, wadda ya ce an tsare ta a wani sansanin soji da ke kusa da birnin Akurdet na yammacin kasar, bayan da aka kama ta tana kokarin tsallaka iyakar kasar. Mutumin ya ce, ‘’iyalan sun dade ba su ji daga gareta ba. Yanzu ta bata.’’ Wasu kafofi sun ce ana barazana ga jami’ai da su dauki tsattsauran mataki a kan wadanda suka nemi gudu, inda ake kai su wurare masu tsanani. Kungiyoyin kare hakkin dan-Adam sun ce, gwamnatin na gudanar da cibiyoyin tsare jama’a inda ake tsare mutane tsawon shekaru ba tare da an bi ka’ida ba. A cikin shekara 28 da ta samu ‘yancin kai daga Ethiopia, Eritrea kusan ta yi yaki da dukkanin makwabtanta - Yemen a 1995, Sudan a 1996, Ethiopia daga 1998 zuwa 2000 da Djibouti a 2008. Aikin soji na tilas da ‘yan kasar ke yi na tsawon wata 18 ya zama na har sai abin da hali ya yi. A cikin shekaru ashirin da suka gabata dubban matasan Eritrea sun gudu daga kasar domin kauce wa tilasta musu shiga aikin soji. Wata mata ‘yar Eritrear da ke zaune a Italiya ta ce, ‘’halin ya shafi ‘ya’yan dan uwana da ya yi shahada, wadanda na dauke su a matsayin abin dogarona. Sun shiga soja. Ba abin da zan iya cewa said ai kawai in ce Allah Yak are dukkanin matasa.’’

