You are here: HomeAfricaBBC2021 04 26Article 1243399

BBC Hausa of Monday, 26 April 2021

Source: BBC

Eric Bailly: Zai ci gaba da wasa a Old Trafford zuwa karshen kakar 2024

Mai tsaron bayan Manchester Eric Bailly ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a kungiyar zuwa karshen kakar 2024.United,

Mai shekara 27 dan kwallon tawagar Ivory Coast ya yi wa kungiyar wasa 100 tun komawarsa Old Trafford daga Villareal a 2016 kan fam miliyan 30.

Sai dai dan wasan ya kan yi fama da jinya a lokacin da yake buga wasanninsa a Ingila.

''Ina cikin farin ciki. Ban dauki lokaci ba wajen yanke hukuncin rattaba hannu kan kwantiragi ba - Ina kaunar kungiyar nan, ina kuma jin dadi buga tamaula a United. '' kamar yadda ya fada.

''Yanzu da zarar na ji sauki zan koma kan ganiyata, shi ne abin da ke gabana. Sabuwar kwantiragi kamar sabon kalubale zan fuskanta kuma a shirye nake.

Sabuwar yarjejeniyar da Bailly ya saka hannu wadda za ta kare a karshen kakar 2024 ta hada da za a iya tsawaita ta kaka daya idan ya ci gaba da taka rawar gani.