You are here: HomeAfricaBBC2021 03 29Article 1218184

BBC Hausa of Monday, 29 March 2021

Source: bbc.com

Cutar korona: Ko riga-kafin korona na jabu ya shiga Najeriya?

Gwamnatin Nijeriya ta ce zuwa yanzu babu wata shaida da ke nuna cewa an shigar da allurar riga-kafin cutar korona ta jabu da ake zargin wasu sun yi safararta daga China zuwa Nahiyar Afirka.

Wata sanarwa da ma'aikatar lafiyar Najeriya ta fitar ta ce an kama irin wannan allurar riga-kafi a China, sannan har an samu rahotanin ɓullarta a wasu kasashen Afrika.

Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta ƙasar dai umarci manyan daraktocin cibiyoyin kiwon lafiya a duk fadin kasar da su sa ido don tabbatar da cewa rigakafin bai shigo Najeriya ba.

A cikin wata sanarwar Daraktan kula da asibitoci na ma'aikatar, Dr Adebimpe Adebiyi, ma'aikatar ta ce ta samu wasika daga kwamitin da shugaban kasa ya kafa don yaki da korona, a kan wannan batu na kama allurai 3,000 na rigakafin koronar na jabu wanda aka kama a wasu kasashen Afrika.

An kuma bukaci hukumar kula da shige da fice ta kwastam ta Najeriya ta sanya filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a matsayin hanya daya tilo ta shiga da rigakafin da aka kawo daga kasashen waje.

Latsa lasifiƙar dake sama don jin ƙrin bayanin da babban sakataren a ma'aikatar lafiya ta Najeriya ya yi wa BBC kan wannan batu.

Join our Newsletter