You are here: HomeAfricaBBC2021 05 11Article 1257964

BBC Hausa of Tuesday, 11 May 2021

Source: BBC

Cutar korona: An sake kafa dokar kulle a dukkan jihohin Najeriya daga yau Talata

Shugaba Muhammadu Buhari Shugaba Muhammadu Buhari

Kwamitin shugaban Najeriya mai yaki da annobar korona a Najeriya ya sanar da sake kafa dokar korona da za ta shafi wasu bangarori na rayuwar jama'a, da zummar dakile cutar daga yaduwa.

Daga yau Talata, an rufe gidajen rawa da wuraren motsa jiki da sauransu a dukkanin faɗin jihohin kasar, saboda fargabar sake bazuwar cutar, a dai dai lokacin da ake ganin hakan na faruwa a da-dai lokacin da ake ganin hakan na faruwa a wasu kasashen duniya.

Mahukunta a ƙasar dai sun jaddada matakan kariya ciki har da hana zirga-zirga daga ƙarfe 12n dare zuwa huɗu na asuba.

Sun kuma nanata matakin hana tarukan mutane fiye da hamsin, sannan a wuraren ibada, dole ne rabin mutanen da wuri yake ci ne kawai aka yarda su yi shiga don yin ibadah.

Manajan gudanarwa na kwamitin kula da al'amuran cutar korona na shugaban ƙasa a Najeriyar Dr. Mukhtar Mohammed ta wayar tarho ya bayyanawa BBC cewa baza su jira sai al'amura sun sake dagulewa kafin a fara tunanin me ya kamata a yi ba.

''Mun yi la'akari da irin abubuwan da ke faruwa a kasashen Brazil da Ajantina da Amurka, kai har ma da wasu kasashen Afrika inda ake samun karuwar masu kamuwa da wannan cuta, don haka muka ga dacewar dauakr wannan mataki tun yanzu don kare al'ummarmu'' a cewarsa.

Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar coronavirus

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar numfashi ta coronavirus.

Yaya zan kare kaina daga cutar?

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.