You are here: HomeAfricaBBC2021 10 27Article 1389157

BBC Hausa of Wednesday, 27 October 2021

Source: www.bbc.com

Covid-19: Sanatocin Brazil sun goyi bayan tuhumar Shugaba Bolsonaro

Anyi zangazanga da yawa akan yadda shugaban ƙasar Jair Bolsonaro ya yaki COVID-19 Anyi zangazanga da yawa akan yadda shugaban ƙasar Jair Bolsonaro ya yaki COVID-19

Wani kwamitin Majalisar Dattawa a Brazil ya yi ƙuri'a inda ya bayar da shawarar tuhumar Shugaban ƙasar Jair Bolsonaro kan kan irin riƙon da ya yi wa annobar korona.

Mutum bakwai cikin 11 na kwamitin sun goyi bayan rahoton da aka bayar da ke neman a tuhume shi da laifi tara ciki har da aikata laifukan cin zarafin bil adama.

Mista Bolsonaro dai ya kafe kan cewa shi fa babu wani laifi da ya yi.

Sama da mutum 600,000 ne aka tabbatar da cewa korona ta yi ajalinsu a Brazil, wadda ƙasar ce ta biyu bayan Amurka a yawan mace-mace sanadin annobar bayan Amurka.

Daga cikin zarge-zargen da akae yi wa shugaban, har da almubazaranci da kuɗaɗen ƙasar da kuma yaɗa labaran ƙarya.

Shugaban kwamitin majalisar, Sanata Omar Aziz zai tura abubuwan da kwamitin ya tattauna a yau ranar Laraba.

Babu wani tabbaci da ke nuna wannan hukuncin da kwamitin ya yanke zai kai ga kama Mista Bolsonaro da laifi ganin cewa a yanzu sai shugaban masu shigar da ƙara na Brazil ya duba rahoto da kuma shawarar da aka bayar game da Bolsonaro, kuma Mista Bolsonaron ne ya naɗa shugaban masu shigar da ƙara na ƙasar.

Mai gabatar da rahoton binciken Renan Calheiros ya caccaki Mista Bolsanaro kan laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Sai dai yayin da babban ɗan shugaban ƙasar Flavio Bolsonaro wanda lauya ne yake mayar da martani ga kwamitin majalisar, ya yi watsi da wannan rahoto.

"Wannan rahoton siyasa ce tsantsan tsagwaranta wanda bai da wata makama ta shari'a. Kuma ina jin alamun ramuwa daga ɓangaren mai gabatar da rahoton binciken wato Mista Renan kan irin sunaye marasa daɗi da ya kira Mista Bolsonaro da su a wannan majalisa,"

Ƙuri'ar da yan kwamitin majalisar suka yi, ta kawo ƙarshen binciken da aka shafe wata shida ana yi wanda ya yi bankaɗa kan irin abin kunyar da aka tafka a gwamnatin Brazil.

Tun daga farkon binciken, gwamnatin Mista Bolsonaro ta kafe kai da fata cewa gwamnatinsa ta yi abin da ya dace tun daga farkon ɓullar annobar.