You are here: HomeAfricaBBC2021 06 10Article 1283098

BBC Hausa of Thursday, 10 June 2021

Source: www.bbc.com

Coronavirus: Birane 10 mafi daɗin zama a duniya a 2021

Birnin Auckland na ƙasar New Zealand ne wanda ya fi daɗin zama a duniya Birnin Auckland na ƙasar New Zealand ne wanda ya fi daɗin zama a duniya

Birnin Auckland na ƙasar New Zealand ne wanda ya fi daɗin zama a duniya, a wani sabon rahoto na jerin birane mafiya daɗin zama da ake fitarwa duk shekara, wanda annobar cutar korona ta sa aka ɗage fitar da shi.

Binciken na Sashen Leƙen Asirin Tattalin Arziki wato Economist Intelligence Unit (EIU), ya yi duba ne kan birane 140, kuma yana yin la'akari ne da abubuwan more rayuwa da ilimi da kuma kiwon lafiya.

Amma a wannan shekarar ƙoƙarin daƙile annobar cutar korona ne abin da aka yi la'akari da shi.

Hakan na nufin ƙasashen yankin Turai ba su kai labari ba bana yayin da biranen da ke Australiya da Japan da kuma New Zealand suka mamaye jerin.

Waɗannan ƙasashe sun yi gaggawar shawo kan yaɗuwar annobar cutar korona kuma sun samu damar rage yawan masu kamuwa da cutar tare da sassauta matakan kulle.

Su kuwa ƙasashen Turai sun yi ta yin nawa wajen fara yin riga-kafi sannan da yawansu sun yi ta ƙaƙaba dokokin kullen hana yaɗuwar cutar korona masu tsauri waɗanda suka yi matukar tasiri a kansu a binciken na bana.

Birnin Auckland ne tkan gaba a jerin sannan sai na na Osaka a Japan da Adelaide da Australia da Wellington na New Zealand da kuma babban birnin Japan wato Tokyo.

Babu wani birni a Birtaniya da ya shiga cikin jerin goman.

"Auckland ya zamo na farko ne saboda irin matakan da ya bi wajen tunkarar annobar cutar korona kuma ya yi nasara, wanda hakan ya sa al'ummar birnin suka ci gaba da watayawa ba tare da kulle ba kuma wannan ya sa ta yi zarra," a cewar EIU.

"Ƙasashen yankin Turai a bana ba su yi abin a zo a gani ba," ya ƙara da cewa.

Alal misali birnin Vienna, ya faɗo daga na ɗaya zuwa na 12. Babban birnin Austria kuwa ya shafe shekaru yana shiga cikin jerin, yawanci yana yin kan-kan-kan da Melbourne.

Amma birnin Hamburg a arewacin Jamus ya faɗo warwas daga na 34 zuwa na 47.

Hakan ya faru ne saboda "matsalar rashin wadatattun kayayyakin amfanin asibiti" wanda binciken ya ce ya ƙara jawo taɓarɓarewar fannin lafiya a mafi yawan biranen Jamus da Faransa.

Binciken ya kuma ce matakan kullen hana yaɗuwar cutar korona ya rage jin daɗin zama a biranen.

"Birane a faɗin duniya a yanzu ba su da daɗin zama ba kamar a baya ba kafin ɓullar annobar, kuma mun ga yadda abin ya fi shafar yankuna irin su Turai," a cewar EIU.

A yayin da abin ya sauya a bana kan birane mafi dadin zama, binciken ya ce ba a samu sauyi sosai ba a jerin biranen da ba su da dadin zama.

Har yanzu Damascus ne birnin da ya fi wahalar yin rayuwa a ciki, saboda yaƙin basasar Siriya da ake ci gaba da yi.

Ana fama da rikice-rikice ne a duk yawancin biranen da aka sanya a jerin waɗanda ba su da daɗin zama, lamarin da ke lalata tsarin kiwon lafiyarsu da ababen more rayuwa.


Birane 10 mafiya dadin zama a shekarar 2021

 • Auckland, New Zealand


 • Osaka, Japan


 • Adelaide, Australia


 • Wellington, New Zealand


 • Tokyo, Japan


 • Perth, Australia


 • Zurich, Switzerland


 • Geneva, Switzerland


 • Melbourne, Australia


 • Brisbane, Australia


 • Birane 10 da ba su da dadin zama a shekarar 2021

 • Damascus, Syria


 • Lagos, Najeriya


 • Port Moresby, PNG


 • Dhaka, Bangladesh


 • Algiers, Algeria


 • Tripoli, Libya


 • Karachi, Pakistan


 • Harare, Zimbabwe


 • Douala, Cameroon


 • Caracas, Venezuela