You are here: HomeAfricaBBC2021 10 01Article 1370482

BBC Hausa of Friday, 1 October 2021

Source: www.bbc.com

Carlo Ancelotti na sa ran Karim Benzema zai lashe Ballon d'Or

Karim Benzema, dan kwallon Real Madrid Karim Benzema, dan kwallon Real Madrid

Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti na sa ran Karim Benzema zai iya lashe kyautar Ballon d'Or.

Kyautar dai ta kasance tsakanin Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a shekarun baya da suka dunga bani in baka wajen lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya.

Tuni dai ake ta hasashen rawar da dan kwallon tawagar Faransa ke takawa a bana a wasanin da yake buga wa.

Benzema mai shekara 33 ya fara kakar bana da zazzaga kwallaye takwas ya kuma bayar da bakwai aka zura a raga da hakan ya kai Real Madrud ta daya a kan teburin La Liga, bayan wasa shida.

Dan wasan na sa ran kara nuna kansa ranar Asabar a gasar La Liga fafatawar mako na bakwai a Bernabeu da Villareal za ta ziyarta.

Ancelotti ya ce dan kwallon Faransa yana da damar lashe kyautar Ballon d'Or a irin wannan lokacin da yake taka gagarumar rawa a Real Madrid a kakar nan.

Ancelotti zai buga wasa da Villareal ba tare da fitattu shida na Real Madrid ba, kuma wasan zai yi zafi ganin itama kungiyar Unai Emery ba ta yi rashin nasara ba kawo yanzu, wadda ta ci wasa daya da canjaras hudu.

Ranar Talata Real za ta karbi bakuncin Sheriff a wasa na biyu na cikin rukuni a Champions League.