You are here: HomeAfricaBBC2021 04 01Article 1221451

BBC Hausa of Thursday, 1 April 2021

Source: www.bbc.com

Birnin da ya zama kufai a Libiya saboda 'kisan gillar da ake yi wa mutane'

A matsayinsa na babba a gidan, kuma namiji daya tilo da ya tsira a zuriyarsu, nauyi ya rataya a wuyan Abdel Manaam Mahmoud na yi wa dan uwansa Esma'il sutura da binne shi. Duk da cewa a yau ba dan uwansa zai binne ba.

Mazajen Tarhuna sun kewaye shi, sun yi amfani da hannunsu wajen zuba jar kasa don rufe wani kabari.

A kusa da su an binne Hussin, mahaifin Mahmoud, da dan uwansa Nuri da kuma kawunsa Mohamed, dukka sun mutu a yakin basasar Libya, wadanda lamarin ya rutsa da su, da mayakan sa kai suke da iko da garin suka kashe duk a kokarin karbar iko.

An gano gawawwakinsu ne bayan rattaba hannu a yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a a shekarar da ta gabata.

Tun bayan hambarar da gwamnatin marigayi Mu'ammar Gaddafi a shekarar 2011, kasar ta shiga rudani, daga bisani kuma ta fada cikin yakin basasa.

Yakin ya kara munana ne cikin shekarun nan bayan Janaral Khalifa Haftar mai shekara 77 da magoya bayansa suka kai zafafa kai hare-hare a gabashin birnin Benghazi tare da kokarin hambarar da gwamnatin da kasashen duniya suka aminta da ita a birnin Tripoli.

Haftar yana da manyan magoya baya kamar kasashen Syria, da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Jordan da kuma Faransa.

Hare-haren da yake kai wa Tripoli sun yi rauni bayan da Turkiyyar ta kai wa gwamnatin da ke gabashin Libya gudunmawar sojoji da jirage marasa matuka.

Kari kan lamarin shi ne makaman yaki da ita ma Syria ta taimaka wa gwamnati da take karkashin jagorancin Kurdawa.

A nasa bangaren Haftar shi ma yana da manyan makamai daga Rasha, ga kuma mayaka da ke taimaka masa daga kasashen Sudan da Chadi.

Amma an cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta, kuma a karon farko cikin shekaru Libya ta samu dunkulalliyar gwamnati.

Firai ministanta shi ne Abdul Hamid Dbeibah, attajirin dan kasuwa da ya fito daga Misrata. Duk da iyalansa na da 'yar alaka da gwamnatin marigayi Mu'ammar Gaddafi, ba a san wasu bayanai game da sabon Firai ministan ba ko sabon dan siyasar ba.

Wani jami'in diflomasiyya Mista Dbeibah da Majalisar Dinkin Duniya ta nada a matsayin mai shiga tsakani a kafa gwamnatin hadaka, ya ce firai ministan bai yi fice ba, don haka babu bangaren da zai karkata.

Ana sa ran nan da watanni tara za a yi zabe a kasar, a ranar 24 ga watan Disamba da ta zo daidai da ranar da Libya ta samu 'yancin kai, sai dai a hakan ma ana tababar yiwuwar zabe a lokacin.

"An ba da ƙurarren lokaci, kuma ba lallai a cimma lokacin ba. Amma duk da haka za a fara ne da dukkan bangarori da hukumomin Libya," in ji Jan Kubis jami'in Majalisar Dinkin Duniya a kan sha'anin Libya.

Bayan tattaunawarmu, Mista Kubis ya wuce Benghazi domin gana wa da Janaral Haftar, mutumin da yawancin mutanen Tarhuna suka yi amanna da kafa kungiyar Seven Kano Brothers, da Mahmoud ya zarga da kashe 'yan uwansa a kashe-kashen da suka yi gabannin barin garin.

Wasu na zargin janaral din da bai wa 'yan uwan da suka tsira mafaka, wadanda suke cikin jerin wadanda Amurka da Tarayyar Turai ta sanyawa takunkumi.

An binne mutum 13 a makabartar garin. Maza da samarin garin sun zo cikin shiri, daruruwansu sun yo tattaki bayan an kammala Sallar Juma'a, wasu daga ciki sun yi amfani da sallaya don kare kansu daga tsananin ranar da ake kwallawa.

Bayan kammala binne mamatan, Mahmoud ya ce; ''Sun dauke min 'yan uwa daga gidajensu, farar hula ne. A watan Oktobar bara, mayakan sa kai na al-Kani sun shigo har gida cikin motocin gwamnati, suka kwashe su baki daya tare da kashesu.''

Ya shafe watanni 10 yana neman 'yan uwansa, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba. Da farko gawar Hussi, da Nuri da Mohamed aka fara gani. Watanni biyu da suka wuce aka gano gawar Esma'il.

"Ko Gaddafi cikin shekaru 42 na mulkinsa, bai yi irin kashe-kashen da muke gani a yanzu ba. A matsayinmu na farar hular Libya, ba mu da masu kare mu, an sarayar da rayuwarmu,'' in ji Mhmoud.

Kungiyar Kani da ta yi fice bayan sace zakuna uku a gidan ajiye namun daji da ke Tripoli, suke kiwo a gida, ita ke iko da fannin shari'ar Libya, sun mulki Tarhuna a lokacin yakin basasar.

Mulkinsu ya zo karshe a watan Yunin bara, lokacin da dakarun gwamnati da taimakon sojojin Turkiyya suka karbe iko da garin.

Turkiyya ta aike da jiragen yaki bakwai ta tekun kasar don fatattakar mayakan Haftar, da kawo dubban mayakan Syria daga yankin Idlib, Aleppo da Deir Ezzor don su yake su ta kasa.

A lokacin fafatawar ne sauran Kani da ba su mutu ba da iyalansu suka tsere zuwa gabashin kasar da babu wanda ya san inda suke.

An yi wa makabartar Tarhuna tsari irin na addinin usulunci, kewaye take da bishiyoyi da allunan da aka rubuta sunayen mamata a jikin kabarinsu, amma a kabarin Esma'il an rubuta lambar kwayar halittarsa ta DNA: 051-000066.

An yi haka ne saboda ba lallai ne gawar da aka binne ta Esma'il ta kasance tasa ce ba. An gano gawarsa ne ta tufafin da yake sanye da su a jikinsa a lokacin da aka gano gawawwakin da aka binne a kabari guda a kudancin birnin.

Hanyar zuwa gidan gona kewaye take da gyadar almond. An rubuta ''Babu mai shiga, sai kwamitin mutanen da suka rasa 'yan uwansu'' a jikin allon shiga.

A bayan gidan gonar akwai tarin jar kasa a nan da can. Suna da yawa ba za ka iya kirgasu ba, manya da kanana.

Yau Juma'a don haka babu aiki, wurin ya yi tsit, amma duk wata shaida da za ta nuna an gudanar da muggan ayyuka a wajen ta bayyana.

A wani rami daya an sanya alamar abu hudu da ke nuna ta yiwu mutum hudu ne a ciki da aka nanndesu tare, da kyar ka shaida fuskokinsu.

An binne mata da maza da yara a wajen, wadanda aka harba akai, jikin wasu daga ciki sun nuna an azabtar da su.

Busasshiyar kasar ta sanya gawawwakin ba su rube sosai ba, sun dan kumbura, abin akwai tashin hankali.

Za a tabbatar da gawar Esma'il ne idan sakamakon gwajin kwayar halitta ya fito na dakin gwaji da ke Tripoli.

Kawo yanzu hukumomin gwamnati da ke jagorantar shirin gano wadanda suka bata sun ce an gano gawawwaki 140. Tuni aka gano mutum 22 daga cikinsu.

Mutane 350 ne suka bata a garin, ta yiwu an binne gawarsu a wani wuri da ba a sa ni ba. A Libyan an kai rahoton batan mutum 6,000 tun bayan faduwar gwamnatin marigayi Muammar Gaddafi, kuma mutane 1,950 kadai aka gano.

A tsaye a cikin makabartar mun ga Ahmad Abdel-Mori Saad, wanda ya zo binne abokinsa, ya shaida mana Tarhuna ta zama kufai.

"Ina da 'yan uwa bakwai da Kaniyat suka sace, mun binne biyu daga ciki da muka gano a kabarin da aka binnesu."

Mista Saad bai san inda sauran 'yanuwansa suke ba, amma ya yi amanna sun mutu. An bar shi da kula da 'ya'ya 24 da suka bari.

"Ba ma bin wata jam'iyyar siyasa, mu ba sojoji ba ko 'yan sanda, idan kana da kudi mutuwa za ka yi, idan kana tattaunawa da ni, mutuwa za ka yi, idan ba ka taimaka min, mutuwa za ka yi.

"Idan kana da 'yan uwa, nan ma mutuwa za ka yi.

Kowa mutuwa yake yi, babu laifin tsaye bare na zaune, kashe mutane kawai suke."