You are here: HomeAfricaBBC2021 04 06Article 1225498

BBC Hausa of Tuesday, 6 April 2021

Source: BBC

Bahaushiya ta farko a majalisar kasar Sudan ta bayyana irin ƙalubalen da ta fuskanta a matsayin yar siyasa

Wata Bahaushiya kuma ƴar siyasa a Sudan, Maryam AbdulKareem Muhammad Ahmad wadda asalinta malamar makaranta ce, amma ta shiga harkokin siyasa tun daga matakin jiha ta shaida wa BBC yadda aka yi ta shiga siyasa da irin gwagwarmayar da ta sha.

An fara zabarta ga muƙamin ƴar majalisar jiha kafin daga baya aka zaɓe ta zuwa majalisar ƙasar a matsayin ƴar majalisar dattawa, wanda ita ce mace Bahaushiya ta farko da ta taɓa riƙe wannan muƙamin a Sudan. 

Ta kwashe tsawon shekaru biyar a majalisar dattijan ƙasar kafin kifar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar Al Basheer.

A tattaunawarsu da wakiliyar BBC Fauziyya Kabir Tukur a Khartoum babban birnin na Sudan, Maryam AbdulKareem Muhammad Ahmad ta bayyana yadda Hausawa ke rayuwa da ma wasu batutuwan da suka shafi Hausawan na Sudan.

Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa domin sauraron cikakkiyar hirar: