You are here: HomeAfricaBBC2021 03 29Article 1218310

xxxxxxxxxxx of Monday, 29 March 2021

Source: www.bbc.com

An yi wa mutum kusan dubu 400 allurar rigakafin korona a Najeriya

Kusan makonni uku bayan da Nijeriya ta soma yi wa al'umarta allurar rigakafin cutar korona, mutum sama da dubu 370 ne suka karbi rigakafi na farko.

Alkaluman da hukumar kula da lafiya a matakin farko ta fitar sun nuna cewa adadin wadanda aka yi wa allurar ya kai dubu 374,585 a ranar Juma'a.

Alkaluman na hukumar ta NPHCDA sun nuna cewa dukkanin jihohi da ke kasar ban da jihar Kogi sun kaddamar da shirin rigakafi a kan annobar korona wadda ta yi sanadin mutuwar mutum sama da dubu biyu a kasar.

Ba a samarwa jihar Kogi da allurar ba saboda ana kan gyaran wurin adana rigakafin da aka lalata lokacin zanga-zangar EndSARS in ji shugaban hukumar, Dr Faisal Shu'aib.

Alkaluman sun nuna cewa, jhar Legas wadda ita ce matattarar masu korona a Nijeriya ta yi wa kusan mutum dubu 92 rigakafi, sai jihar Ogun wadda ta yi wa mutum sama da dubu 36.

Jihar Bauchi ita ce ta uku da mutum sama da dubu 31 yayin da jihar Kaduna ita ce ta hudu da mutum sama da dubu 29.

Jigawa ta yi wa mutum sama da dubu 222 yayin da Kwara ta yi wa mutum sama da dubu 20.

Jihohi masu mutane kalilan da aka yi wa rigakafi sun hada da Kebbi da Taraba da kuma Abia.

A farkon watan da mu ke ciki ne Najeriya ta karbi allurar rigakafin korona ta kamfanin Oxford AstraZeneca miliyan 3.94.

Join our Newsletter