You are here: HomeAfricaBBC2021 09 15Article 1357345

BBC Hausa of Wednesday, 15 September 2021

Source: www.bbc.com

An bar Afirka a baya a rigakafin korona — WHO

Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, Babban Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, Babban Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya

Babban Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya, ya koka da cewa a cikin allurar riga-kafi fiye da biliyan biyar da miliyan 700 da aka yi wa al'ummar duniya, kashi biyu na wannan adadi ne kaɗai aka yi wa mutanen Afirka.

Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce hakan ba kawai raunata al'ummar Afirka ya yi ba, abu ne da ya raunata dukkaninmu.

A cewarsa matuƙar aka ci gaba da nuna rashin dai-daito wajen samar da allurar riga-kafin korona, ƙwayoyin cutar za su yi ta rikiɗa tare da zagaya a tsakanin al'ummar duniya, lamarin kuma zai ci gaba da kawo cikas ga harkokin tattalin arziƙi da na zamantakewa, baya ga yi wuwar samun hayayyafar ƙarin nau'o'in korona da za su dakushe tasirin alluran riga-kafin da ake da su.

Dr Tedro Ghereyesus na tare da Dr Seth Berkley, jagoran shirin Gavi da jakadan cutar korona na musamman daga Tarayyar Afirka Strive Masiyima da Dr. John Nkengasong Daraktan Cibiyar Daƙile cutuka masu yaɗuwa da sauran manyan jami'ai.

Sun kuma nanata burin Hukumar Lafiya ta Duniya na yi wa kashi 70 cikin 100 na al'umma a dukkan ƙasashe allurar rigakafin kafin nan da zuwa tsakiyar shekara mai zuwa.

Strive Masiyima, ya ce rabon allurar rigakafin abu ne mai kyau, to amma kuma bai kamata kasashe su dogara kacokan a kan rabon allurar ba, ya kamata su duba yi wuwar yadda za su sayi ta su.