You are here: HomeAfricaBBC2021 09 08Article 1352263

BBC Hausa of Wednesday, 8 September 2021

Source: www.bbc.com

Afghanistan: 'Yan Taliban sun rungumi shafukan sada zumunta

Yan Taliban sun cire gwamnatin Ashraf Ghani ayayin da suka shigo babban birnin Kabul Yan Taliban sun cire gwamnatin Ashraf Ghani ayayin da suka shigo babban birnin Kabul

A farkon watan Mayu, yayin da dakarun Amurka da Nato ke ficewar karshe daga Afghanistan, Taliban ta zafafa kai hare-hare akan dakarun Afghanistan da ke ba da tsaro.

Sai dai kuma sun kaddamar da wani shiri da ya sha bamban da wanda aka sani a baya - domin sun kaddamar da shafukan sada zumunta domin yada manufofinsu.

Shafukan sada zumuntar na nuna gazawar gwamnatin Kabul da zuzuta nasarar Taliban.

A wani martani, mataimakin shugaban Afghanistan Amrullah Saleh ya gargadi dakarunsu da al'umma kan fadawa ko amincewa da labarin karya da boge da Taliban ke yayatawa a shafukan sada zumunta.

Bayanai na nuna cewa Taliban ta sauya lamuranta da aka sani a baya inda yanzu ta rungumi sabbin tsare-tsare da ci gaban fasaha.

Lokacin da Taliban ta hau mulki karon farko a 1996 a Afghanistan, sun haramta amfani da intanet da haramta ko lalata talabijin, kamarori da faya-fayan bidiyo.

A 2005, aka kaddamar da Shafin Taliban na Al-Emarah, wadda a yanzu ke yada labarai a harsuna biyar - Ingilishi da Arabiya da Pashto da Dari da Urdu.

Abubuwan da shafukan ke yadawa na murya da bidiyo da rubuce-rubuce na gudana ne karkashin jagorancin hukumar addini na Taliban da Zubihullah Mujahid ke jagoranta.

A baya an dakatar da shafin Twitter din Zabihullah Mujahid, amma shafinsa na yanzu da ke aiki tun 2017 na da mabiya sama da 371,0000. Sannan akwai masu ra'ayin taimaka wa ayyukan Taliban a kyauta da ke bibiyar shafinsa.

Mr Mujahid ya shaida wa BBC cewa mayakan na da tawaga da suka kasafta a kowanne ɓangare a Twitter - a kokarin ganin maudu'in Taliban ya ja hankali - da kuma tura sakonni a WhatsApp da Facebook.

"Makiyanmu na da tashar Talabijin da rediyo da shafukan da aka tantace a soshiyal midiya, mu kuma bamu da ko guda kuma muna yaƙi da su a Twitter da Facebook kuma mun yi nasara." a cewar Mujahid.

Akwai mutum miliyan 8.6 da ke amfani da intanet a Afghanistan, don haka rashin intanet da data manyan kalubale ne.

Taliban ta ce tana biyan tawagarta ta soshiyal midiya kowanne mutum dala 11.51 a wata domin yi musu yaƙi a shafukan sada zumunta, a cewar Mr Muhajid.

Ya yi ikirarin cewa Taliban na da hadaddun sutudiyo hudu da suke ayyukansu na tattara murya da bidiyo domin yadawa a intanet.

Ya ce ana iya ziyararta shafukan domin ganin sakamakon da ke nuna yada mayakan Taliban suka samu nasara kan mayakan ketare da na kasa, komai na sanye a shafinsu na Youtube da Al-Emarah.

Kungiyar na wallafe-wallafenta kai tsaye a Twitter da Youtube, sai dai Facebook ya taka mata burki. Facebook ya ce zai ci gaba da haramta duk wani abu da ke da alaka da Taliban a shafinsa.

Mujahid ya shaida wa BBC cewa Taliban ta gamu da cikas wajen gudanar da ayyuka a Facebook, abin da ya sa ta mayar da hankali akan Twitter.

Duk da cewa ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana kafar sadarwar Haqqani a matsayin kungiyar 'yan ta'adda a duniya, shugabansu Anas Haqqani da sauran mambobin kungiyar na da shafin Twitter da dubbai ke bibbiya.

A lokacin wasu bayanai da bukatar sakaya suna, ɗaya daga cikin mambobin Taliban a shafukan sada zumunta ya shaidawa BBC cewa mayakan sun yanke hukunci amfani da Twitter tallata makalar da New York Times ta wallafa, wanda Sirajuddin Haqqani ya rubuta, mataimakin shugaban Taliban, a Fabrairun 2020. Akasarin shafukan da ake gani a Twitter na Taliban a lokacin aka kirkiro su.

"Akasarin 'yan Afghanistan ba sa jin Turanci, amma shugabanninsu da ke mulki a Kabul na magana da Turanci a Twitter - saboda mulkinsu ba iya kasar kadai ya tsaya ba," a cewarsa.

"Taliban na don yakar farfaganda a kanta, shiyasa take habbaka kanta a Twitter."

Ya ce mambobin Taliban, da ke da dubban mabiya, an fidda musu sharuda " kar su yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi harkokin ketare da kasashe makwabta, da ke iya yanke alaka da su".

A baya, an san Taliban da sirri kan bayyana kansu da bayanan shugabanninsu da mayaka. Abin ya kai matsayin da su na boye fuskar mutumin da ya samar da kungiyar, Mullah Omer.

A yau, a kokarin samun karbuwa a duniya, shugabanni ba su tsaya kan bayyanai a kafofin yada labarai ba, abin ya kai ga suna tallata kansu da ayyukansu a shafukan sada zumunta.

Lokacin da kakakinsu, Zabihullah Mujahid ya zanta da manema labarai kan nasarar karbe Kabul, fuskar shafukan Twitter mayakan da dama ta koma hotonsa.

Wani abu na daban shi ne a yanzu, 'yan Afghanistan da dama da ke aiki da dakarun kasa da kasa da kungiyoyi da kafofin yada labarai da masu sukar Taliban a shafukan sada zumunta a yanzu na goge shafukansu, saboda fargabar rayuwarsu na iya shiga barazana.

Kungiyoyin kare hakki na Amnesty da Human Rights Watch sun ce sun karbi rahotanni kan Taliban na bincike da zargin kisa a matsayin martani.

Facebook ya kaddamar ya wani tsari da zai taimaka wa 'yan Afghanistan sauri toshe ko kulle shafukansu, da kare duk wani mutum daga shiga barazana ko samun bayanansu.

Sannan shafin ya ce ya cire damar da ke bai wa mutum iya binciko ko duba abokansa ko mutanen da ke amfani da shafin Facebook a Afghanistan.

Abin tambaya a yanzu shi ne, ko Taliban ta sauya manufofinta da jingine cin zarafi da ake alakanta da su.

Da dama daga cikin 'yan Afghanistan da sauran al'ummar duniya ba su yarda da cewa za su sauya alkawarinsu ba.

Sai dai babu shaka rungumar fasahar zamanin da a baya suka bijirewa ya iya taimakawa wajen sauya tunaninsu a matakin duniya baki daya.

"Shafukan sada zumunta na da karfi musamman wajen sauya tunanin al'umma," a cewar tawagar mambobin Taliban. "Muna son sauya tunanin mutane kan Taliban a duniya."