You are here: HomeAfricaBBC2021 04 29Article 1246075

BBC Hausa of Thursday, 29 April 2021

Source: BBC

Abin da ya sa mata baƙaƙen fata suka fi fararen fata yawan ɓarin ciki

Doreen Thompson-Addo ta yi ɓari sau bakwai a rayuwarta Doreen Thompson-Addo ta yi ɓari sau bakwai a rayuwarta

Mata bakaken fata sun fi fuskartar hadarin yin ɓari a kan fararen fata.

Binciken da mujallar Lancet ta yi kan masu ciki miliyan 4.6 a kasashe bakwai ya nuna cewa idan mace baƙa ce tana fuskantar hadarin yin ɓari da kashi 43 cikin ɗari.

Lancet ta bukaci da a rika bai wa bakaken fata da ke Birtaniya taimakon da ya kamata a duk lokacin da suka yi ɓari.

A yanzu ana yi wa matan bincike na musamman ne kawai idan sun yi ɓari sau uku a jere.

Kuma mafi yawan kasashe da suka hada da Birtaniya ba sa mayar da hankali wurin karɓar ƙididdiga.

Amma binciken masana ya nuna cewa kashi 15 na ciki da ake dauka yana zubewa, yayin da kashi daya na mata ke fuskantar sake ɓari a jere.

Bugu da ƙari an fi samun ɓarin ciki a wasu kasashen a kan wasu, amma kuma ya danganta da yadda kasashen suka fahimci ɓarin kama daga shigar ciki zuwa awo.

Rahoton ya kuma gano cewa matan da suka fuskanci ɓari sun shiga haɗarin kamuwa da rashin lafiya da ake iya daɗewa ba a warke ba, kamar daskarewar jini da ciwon zuciya da kuma tsananin damuwa.

Doreen Thompson-Addo ta yi ɓari sau bakwai a rayuwarta.

"A lokacin da na samu cikina na farko na yi murna sosai", a cewar Doreen.

"Na sanar da yan uwa da abokaina, har ma na fara tunanin sunan da zan saka wa jaririna da sauran shirye-shirye."

Sai dai watanni biyu bayan haka Doreen ta fara zubar jini daga nan kuma ta yi ɓari.

A cewar Doreen "za ka riƙa jin labarin ɓari akai-akai, to amma ba za ka taɓa tunanin zai zo kanka ba."

Doreen, wadda ta haifi ƴarta Arielle a 2017, ta samu shawara daga likita a lokacin da ta yi ɓarin farko cewa "ta sake gwadawa."

Amma bayan ta yi ɓari a karo na uku ne aka tura ta wani asibitin kwararru kan ɓari, duk da haka ba ta samu bayanin abin da ya sa ta riƙa ɓari a jere ba.


Abubuwan da ke haifar da ɓari

  • Idan mace ba ta kai shekaru 20 ba ko kuma ta haura 40
  • Idan mace ta taɓa ɓari a baya
  • Mata sirara da kuma masu kiɓa sosai
  • Shafe awanni masu tsawo wurin aiki da kuma aikin dare
  • Mace baƙar fata
  • Mace mai shan taba
  • Mace mai shan giya sosai

Wane irin taimako ake iya basu?

  • Binciken da mujallar Lancet ya ba da shawarar cewa:
  • Taimakon gaggawa tun kafin mace ta samu ciki
  • Yin awo akai-akai da zarar ciki ya shiga
  • Yin hoton ciki don fahimtar halin da yake ciki
  • Kula da kwayoyin halitta
  • Shan magunguna da allurai da za su rage daskarewar jini
  • Gwaji da kuma shan magunguna da zarar an samu zubar jini

Mafi yawan binciken an gudanar dashi ne a kasashen Sweden da Finland da Denmark wadanda sun yi kokarin haɗa kan ƙididdigar da aka gudanar a kasashensu.

Amma duk da haka an yi amfani da bayanai daga kashashen Amurka da Birtaniya da Norway da kuma Canada.

"Mun fahimci cewa akwai karuwar hadarin cewa baƙaƙen fata za su mutu saboda daukar ciki", a cewar Farfesa Siobhan Quenby, ta cibiyar nazarin kan ɓari da ke jami'ar Warwick ta Birtaniya.

"Kuma na kadu matuƙa da na gano cewa ana samun karuwar ɓarin ciki." in ji Farfesa Quenby.

Baƙaƙe sun fi faɗawa hadarin kamuwa da ciwon suga da kuma zuciya, kuma dukansu cutuka ne da ke jefa mace cikin hadarin zubewar ciki.

To amma Farfesar ta ce masana na kan bincike don gano ko cutar ƙabar mahaifa na iya haifar da ɓari.

Sauyin halin rayuwa

Kusan kashi 75 na matan da suka yi ɓari za su zo su sami lafiyayyen ciki daga baya.

Hakan yasa a koda yaushe ake shawartar ma'aurata da su sake gwada samun wanin cikin ba tare da gudanar da binciken musabbabin ɓarin ba.

To amma a cewar Farfesa Quenby akwai abubuwan da za a yi da zasu hana ɓari.

''Ba matsala bace da ake yanke ƙauna.''

Sauya yadda ake tafiyar da rayuwa na hana ɓari da kashi 30.

A cewar Farfesa Quenby da dama daga wadanda ke zuwa asibitinta suna shan sigari, ga su kuma da ciwon suga ko kuma hawan jini.

''Hakan na nufin lafiyar kanta ba ta gama zama ba a jikin mace ballantana ciki ya zauna.'' inji Farfesa Quenby.

Akan haka ta kasa matakan shawo kan matsalar kamar haka:

  • Neman shawara bayan ɓari na farko
  • Sake yin gwaje-gwaje bayan ɓari na biyu
  • Tsananta bincike idan akayi ɓari na uku.
Daga nan kuma mujallar Lancet ta ba da shwarwarin cewa:

Dole ne a samo sabbin hanyoyin shawo kan matsalar.

Kuma zamanin cewa macce ta sake gwadawa ya wuce.

'Mawuyacin hali'

Wani abu da binciken ya koma ganowa shine ƙaruwar mata da ke kashe kansu da kuma shiga tsananin damuwa bayan mace ta yi ɓari.

Bayan ta yi bari sau takwas, Charlotte na sa ran samun tagwaye, to amma bayan an yi mata hoto an gano cewa cikin ya zube.

"Na samu kaina cikin mummunan yanayi."

"Mijina yana ta rarrashina amma bana ji."

"Na ma gaji da rayuwa kwata-kwata.''

'Damuwa bayan ɓari'

Da farko Charlotte ta rungumi ƙaddara.

Kuma a lokacin da ta fara tunanin kashe kanta ta samu taimakon da ya gabata.

Daga baya kuma ta samu haihuwar ɗa namiji bara mai suna Ansel, kuma a yanzu ta na jin cewa a shirye take ta rika magana da sauran mutane kan halin da ta samu kanta.

"Abun farin ciki ne da na samu ɗa," in ji ta.

"Na san ba ƙaramar sa'a nayi ba,"

''Da dama ba su samu irin haka ba."