You are here: HomeAfricaBBC2021 06 10Article 1283035

BBC Hausa of Thursday, 10 June 2021

Source: www.bbc.com

Abin da ya sa Kim Jong-un ya haramta amfani da kaya da fina-finai daga yammacin duniya

Shugaban kasar Kim Jong-un ya kara matsa lamba matuka a kasar Shugaban kasar Kim Jong-un ya kara matsa lamba matuka a kasar

Koriya ta Arewa ta ƙaddamar da wata sabuwar doka mai tarin iko da ke son kawar da dukkan wasu halaye na kasahen waje a cikin kasar - kuma akwai hukunci mai tsanani ga duk wadanda aka samu tare da fina-finan kasashen waje, ko kayan sawa ko ma yin magana da salon harshen wasu al'umomin kasashen ketare.

Wata mata mai suna Yoon Mi-so ta ce yayin da ta ke mai shekaru 11 da haihuwa, ta taba ganin yadda aka kashe wani mutum saboda an kama shi da wani wasan kwaikwayo na Koriya ta Kudu.

An tara dukkan makwabtan mutumin a unguwar da ya ke zaune domin su kalli kisan da aka yi ma sa.

"Idan ka ki halartar kisan, za a iya kama ka da aikata laifin cin amanar kasa," kamar yadda ta shaida wa BBC daga gidanta da ke birnin Seoul na Koriya ta Kudu.

Dakarun Koriya ta Arewa sun rika jaddada wa 'yan kasar cewa hukuncin fasa-kwaurin bidiyon shirye-shiryen talabijin zuwa cikin kasar daga waje laifi ne da hukuncinsa kisa ne.

"Sun daure shi a jikin wani turke, sannan su ka harbe shi."

'Yaƙin da babu makamai'

Yi tunanin rayuwar da a ke wa al'umma kulle babu hutu, babu intanet, babu shafukan sada zumunta, sai dai tashoshin talabijin ƙalilan mallakin gwamnati wadanda aikinsu kawai shi ne a sanar da kai abin da gwamnatin kasar ke son ka sani - wannan ne yadda ainhin rayuwar 'yan Koriya ta Arewa ta ke.

Yanzu kuma Shugaban kasar Kim Jong-un ya kara matsa lamba matuka, inda ya fitar da wasu matakan da hukumomin kasar su ka bayyana a "dokar da za ta yaki miyagun tunani".

Kasar Koriya ta Arewa sai kara janyewa ta ke yi daga hulda da kasashen waje, inda a bara ta kulle iyakointa saboda annobar korona kuma har zuwa yanzu ba ta bude su ba.

Sai dai abin ba ya tsaya ne kawai kan abubuwan da mutane ke kallo ne ba.

A kwanan bayan Mista Kim ya aika da wata wasika da aka wallafa a kafofin yada labarai na kasar inda ya bukaci a fara yakar abin da ya kira "miyagun halayen kin al'umma da son kai" tsakanin matasan kasar. Yana son kawo karshen amfani da harsunan kasashen waje, da salon aski da kayayyakin sanyawa wadanda ya bayyana su a matsayin "guba mai hatsari".