You are here: HomeAfricaBBC2021 06 10Article 1283038

BBC Hausa of Thursday, 10 June 2021

Source: www.bbc.com

Abin da ya kamata ku sani kan kidayar jama'a a Najeriya

Najeriya na gudanar da wani aikin ƙidayar jama'a da gidaje na gwaji a sassan ƙasar Najeriya na gudanar da wani aikin ƙidayar jama'a da gidaje na gwaji a sassan ƙasar

A makon gobe ne - ranar Litinin, Najeriya za ta fara gudanar da wani aikin ƙidayar jama'a da gidaje na gwaji a sassan ƙasar.

Hukumar ƙidaya ta Nijeriya ta ce aikin ƙidayar, na gwaji ne a shirye-shiryenta na tunkarar ƙidayar da ke tafe, abin da zai ba ta damar kintsawa sosai.

Alhaji Nasir Isa Kwara, shugaban hukumar ya shaida wa BBC cewa za a fara ƙidayar gwajin ta hanyar amfani da kwamfutocin hannu saɓanin a baya da aka yi amfani da takardu.

Ya ce za su yi gwajin ne domin hakan zai ba su damar gano duk wata matsala gabanin gudanar da ainihin kidayar - "ko akwai bukatar a yi wasu sauye-sauye da masu yin aikin kidayar ko sun kware wajen yin aikin".

Ya kara da cewa za a bi gidajen da aka dauki hotunansu da tauraron dan adam inda za a yi wa mazauna gidajen tambayoyi game da yawansu da jinsinsu da shekarunsu.

A cewarsa, bayanan da ma'aikatansu suka tattaro za a yi amfani da su wajen shirya babbar kidayar jama'a ta kasa.

A bayanin da ya yi, shugaban hukumar kidaya ta Najeriyar ya ce za a gudanar da kidayar gwajin a duk kananan hukumomin Najeriya ƙasar.

Sai dai a cewarsa, za a yi kidayar gwajin ne a wurare 222 cikin kananan hukumomi 112 har da babban birnin kasar.

Da ya ke magana kan shawarar Majalisar Dokokin Najeriya na a jingine gudanar da kidayar saboda batun tsaro, Alhaji Nasir Isa Kwara ya bayyana cewa "duk wani dan Najeriya da yake ganin abin da ke faruwa a kasar dole ya damu".

Ya ce duk da sun gamsu da shawarar dan majalisar da ya gabatar da wannan kudiri a zauren majalisar amma rashin yin kidayar babban illa ne saboda kidayar za ta taimaka wajen fito da duk wasu abubuwa na ci gaban kasa.