You are here: HomeAfricaBBC2021 05 05Article 1251526

BBC Hausa of Wednesday, 5 May 2021

Source: www.bbc.com

APC da PDP: Wa ce jam'iya ce ta fi kawo koma baya a Najeriya tsakaninsu?

APC da PDP ne kawai suka taba mulki a Najeriya tun shekara 1999 APC da PDP ne kawai suka taba mulki a Najeriya tun shekara 1999

Babbar jam`iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta zargi jam`iyyar APC mai mulki da gazawa wajen kyautata rayuwar al`ummar kasar.

PDP ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ya kasa cika alkawuran da ya yi lokacin neman zabe, don haka ya kamata sauya salo ko ya yi murabus.

Amma jam`iyyar APC ta yi watsi da wannan zargin, tana cewa PDP ce musabbabin tabarbarewar tsaro da sauran al`amura a Najeriya, don haka ba ta bakin sukar gwamnati.

Jam`iyyar PDP ta yi zargin cewa jam`iyyar APC ta rabe ne da halin da Najeriya ta samu kanta ta fuskar tsaro shekara ta 2015, har ta yi wa `yan Najeriya kumfar-baki da alwashin magance matsalar, alhali babu wani shirin da ta yi.

Hasali ma a cewar PDP, duk alkawuran da shugaba Buhari ya yi a baka ne kawai, kuma an kai magaryar tukewa a Najeriya, don haka ya kamata ta gusa gefe ya ba da wuri ga masu yi da gaske.

Senata Umar Ibrahim Tsauri shi ne sakataren jam`iyyar PDP na kasa, ya shaida wa BBC cewa "sun yi alkawarin cewa za su kawo karshen rashin tsaro a Najeriya, za su gyara tattalin arzikin kasar, za su yi yaki da cin hanci da rashawa. Idan an duba yanzu za a ga cewa duk abuuwan da aka fada babu daya wanda aka samu ci gaba a cikinsa sai dai ci baya."

"Yau dan Najeirya ba ta me zai yi yake ba, a'a, ta yadda zai kwana lafiya yake yi. Don haka ko dai shugaban kasa ya kafa dokar ta-baci kan tsaro, ko ya kira taron tsaro na kasa: dukkan wani wanda ya taba zama jami'in tsaro ya zo ya bayar da gudunmawarsa, idan haka ta faskara ya yar da kwallon mangwaro ya huta da kuda", in ji Sanata Tsauri.

Jam`iyyar PDP dai ta ce a shirye take ta hada-kai da jam`iyya mai mulki don sama wa Najeriya mafita, tana nuna takaicin cewa, APC ba ta yi amfani da irin shawarwarin da PDP ta yi ta bayarwa a baya ba.

Sai dai jam`iyyar APC a nata bangaren ta yi fatali da zargin da PDP ke yi, tana cewa da ba a san asali kuli ba da sai ya ce da alkama aka yi shi.

APC ta zargi PDP da tabka kura-kuran da suka jefa Najeriya a halin da ta samu kanta na tsananin talauci, wanda a bangare guda ya ta`azzara matsalar tsaro.

Wannan ne ma ya sa APC ke cewa PDP ba ta da bakin magana.

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Maimala Buni shi ne shugaban kwamitin riko na jam`iyyar APC, kuma ya ce "gaskiyar magana ita ce, idan maye ya manta, uwar 'ya ba za ta manta ba."

Ya kara da cea PDP ce silar dukkan matsalolin da Najeriya ta fada a ciki.

"Sun san halin da suka bar kasar nan a ciki. Su suka gadar da wannan rashin tsaro. Lokacin da ake sace fararen mutane ba su suke mulki ba? Ba su suka ki samar wa 'yan sanda da sojoji kayan aiki ba? Ba su suka bar kasar kara-zube suka ki yin abin da ya kamata ba?"

Dangane da tayin da PDP ta yi na kama wa APC don daidaita al`amura a Najeriya kuwa, Gwamna Maimala cewa ya yi irin wannan dauki yi wa kai ne.

A Najeriya an shiga wani hali na tsaka mai wuya, ga matsalar tabarbarewar tsaro, ga kukan zafin yanayi da na aljihu, sakamakon matsin tattalin arziki. Kuma wannan ya sa `yan kasar da dam a ba sa ganin wasu ayyukan more rayuwa da gwamnatin kasar ke ikirarin yi, saboda `yan magana kan ce idan ana kai ba a ta kaya.

A cewarsa: "Ko kana PDP, ko kana kowace irin jam'iyya, ya zama wajibi gare ka ka yi duk abin da za ka iya yi saboda zaman lafiyar kasar nan."

'Kowa ce jam'iyya tana da laifi'

Sai dai a nasu bangaren, masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun bayyana cewa dukkan jam'iyyun biyu babu wacce ta cire wa 'yan Najeriya kitse daga wuta.

Malam Kabiru Sa'idu Sufi, mai koyar da nazarin siyasa a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, ya ce kowace daga cikin jam'iyyun ta yi mulki ne lokacin da ake fuskantar kalubale daban-daban.

Acewarsa, 'yan kasar sun fi yin magana ne a kan abin da ke faruwa a lokacin da ake ciki.

"A zamanin PDP ne aka fara samun tashin bama-bamai a yankuna da dama na kasar nan, ciki har da Babban Birnin Tarayya.

A zamanin nan na APC kuma aka samu yawaitar kashe-kashen 'yan bindiga da kuma sace-sacen mutane a yankuna da dama."

Join our Newsletter