You are here: HomeSports2021 04 03Article 1222945

BBC Hausa of Saturday, 3 April 2021

Source: bbc.com

Jirgin yaƙin sojin saman Najeriya 'ya faɗi' a Borno

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce watakila jirgin nan nata da ya yi ɓatan dabo ranar Laraba a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar faɗuwa ya yi.

Wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na rundunar Air Commodore Edward Gabkwet, ya fitar ranar Juma'a ta ce bayanan sirrin da suka tattara sun nuna cewa jirgin samfurin Alpha Jet (NAF475) yana ɗauke da mutum biyu.

"Ba a san abin da ya haddasa hatsarin ba da kuma inda matuka jirgi biyu suke. Matuka jirgin su ne Flight Lieutenant John Abolarinwa da Flight Lieutenant Ebiakpo Chapele," in ji sanarwar.

Air Commodore Gabkwet ya kara da cewa jiragen sojin sama masu bincike da dakarun sojan sama na musamman da kuma dakarun sojin kasa suna ci gaba da neman jirgin.

"A halin yanzu, rundunar sojin sama ba za ta iya tabbatar da ainihin abin da ya faru ba game da hatsarin. Sai dai tana fatan nan ba da jimawa ba za a gano matuka jirgin," in ji shi.

Tun da farko rundunar sojin saman ta Najeriya ta ce na'urar da ke hango zirga-zirgar jirage da tuntuɓarsu wato radar ta kasa ganin inda wani jirgin rundunar sojin saman ya shiga.

Jirgin yaƙin yana kan wani aiki ne na taimakon dakarun rundunar sojin ƙasa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Air Commodore Gabkwet ya ce "an daina jin ɗuriyar jirgin ne tun ƙarfe biyar na yammacin Laraba 31 ga watan Maris."

"Har yanzu babu wasu bayanai kan inda jirgin ya shiga ko dalilin ɓacewarsa, amma za mu sanar da al'umma da zarar mun gano wani abu," a cewarsa.

Aikin da jirgin ke yi wani ɓangare ne na ci gaba da yaƙi da ƴan ƙungiyar Boko Haram da ake yi.

Rundunar ba ta kuma yi bayani kan ko mutum nawa ne ke cikin jirgin ba.

Jaridar Punch ta ruwaito wani tsohon kwamanda a rundunar sojin saman ƙasar na cewa "idan har aka yi minti 30 ba a ji ɗuriyar jirgin yaƙi ba to za a ayyana cewa wannan jirgi ya ɓata ne."

A watan Fabrairun da ya gabata ma wani jirgin yaƙin rundunar sojin saman ƙasar ya yi hatsari a Abuj kan hanyarsa ta zuwa Minna, inda dukkan jami'ai bakwai da ke cikinsa suka mutu.

Join our Newsletter